An Buga Kugen Siyasa: Pantami Ya Aika da Zazzafan Sako ga 'Yan Takarar Gwamnan Gombe
- Dan takarar gwamnan Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya ce arzikin jihar na al’ummar Gombe ne, ba ganimar siyasar da za a raba ba
- Pantami ya yi alƙawarin samar da ayyukan yi, tallafa wa matasa da manoma, da bai wa ’yan kwangilar cikin gida damar gudanar da ayyuka
- Wasu matasa da ake zargin ’yan APC ne sun tare hanyar Jekadafari da tayoyi tare da cinna musu wuta domin hana tawagar Pantami shiga Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Dan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya gargaɗi al’ummar jihar kan zaɓen ’yan siyasar da yake zargin suna kallon arzikin Gombe a matsayin ganimar siyasa.
Pantami ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a fadar Sarkin Gombe ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026, inda ya ce dukiyar jihar mallakin al’ummarta ce.

Kara karanta wannan
"Ku ce ni da Kwankwaso mun gaza"; Peter Obi ya dauki muhimmin alkawari ga 'yan Najeriya

Source: Facebook
Wane gargadi Pantami ya yi?
Ya ce bai kamata a ɗauki arzikin Gombe a matsayin abin da za a raba tsakanin ’yan siyasa bayan sun yi nasara a zaɓe ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
“Ɗaya daga cikin ’yan takara ya ce idan aka zaɓe shi, zai raba arzikin Gombe a matsayin ganimar yaƙi. Ina son al’ummar Gombe su fahimci cewa jihar nan ba filin farauta ba ce, kuma arzikin cikinta ba ganimar siyasa ba ne.” In ji shi.
Pantami ya ƙara da cewa arzikin jihar na al’ummar Gombe ne, ba wani abu da ’yan siyasa za su mallaka ko su raba yadda suka ga dama ba.
Duk da dai bai ambaci suna ba, ana kalaman na sa shagube ne ga dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyar APC, Jamilu Gwamna.
Alƙawuran Pantami ga al’ummar Gombe
Dan takarar na PDP ya ce abin da yake son yi idan aka zaɓe shi shi ne samar da ayyukan yi ga al’umma, tallafa wa matasa da manoma, da kuma tabbatar da samun takin zamani.

Kara karanta wannan
Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro
Ya bayyana cewa samar da takin zai taimaka wajen bunƙasa noma da ƙara yawan amfanin gona a jihar.
Pantami ya kuma ce bayar da kwangiloli ga ’yan kwangilar cikin gida na daga cikin dabarun da yake shirin amfani da su wajen farfaɗo da tattalin arzikin Gombe.
Ya ce irin wannan dama za ta taimaka musu samun kuɗin shiga, samar da ayyukan yi da faɗaɗa harkokin kasuwancinsu.
A nasa jawabin, jagoran PDP a jihar, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, ya gode wa magoya bayan jam’iyyar bisa fitowa da yawa domin tarbar Pantami da nuna goyon bayansu gare shi.
Shi ma shugaban PDP na ƙasa, Abdurrahman Muhammad, ya buƙaci shugabanni, mambobi da magoya bayan jam’iyyar su haɗa kai, ƙarfafa jam’iyyar tare da yin aiki tare domin samun nasara a zaɓen jihar Gombe.
An tare hanyar shiga Gombe kafin taron
Tun da farko, wasu matasa sun sanya tayoyi tare da cinna musu wuta a kan titin Jekadafari, kusa da gidan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Lamarin ya faru ne a lokacin da Pantami yake kan hanyarsa ta zuwa babban birnin jihar domin halartar taron siyasa ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan
Rashin imani: Yadda 'yan bindiga suka kona mutum 12 'yan gida 1 da ransu a Zamfara

Source: Original
Pantami ya dauki alkawura
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar gwamnan Jihar Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana abubuwan da zai yi wa al'umma idan ya samu nasara.
Farfesa Pantami ya yi alkawarin yaki da talauci, samar da ayyukan yi da tallafa wa matasa, mata, manoma, ’yan kasuwa da ’yan kwangilar cikin gida idan aka zabe shi a 2027.
Asali: Legit.ng