Shugaban INEC Ya Tafi Kasar Waje, Ya Fada wa DuniyabMatakin da Za Su Dauka kan Takarar Atiku a 2027

Shugaban INEC Ya Tafi Kasar Waje, Ya Fada wa DuniyabMatakin da Za Su Dauka kan Takarar Atiku a 2027

  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan halascin takarar Atiku Abubakar a 2027
  • Amupitan ya bayyana cewa INEC na fuskantar shari’o’i sama da 300 yayin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke ƙara ƙamari
  • Ya yi kira da a riƙa kammala shari’o’in zaɓe kafin watanni shida ko shekara ɗaya da zaɓe domin bai wa hukumar damar shirya kayayyakin aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

London, United Kingdom - Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar za ta bi duk hukuncin da kotu ta yanke kan takarar Atiku Abubakar, a zaɓen 2027.

Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a Chatham House da ke Landan na kasar Birtaniya.

Kara karanta wannan

Da yiwuwar INEC ta cire Atiku daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa a makon gobe

Amupitan.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan yana magana da manema labarai Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa Amupitan ya amsa tambaya kan ko Atiku zai cancanci tsayawa takara idan ya gaza soke hukuncin kotun da ya shafi shugabancin ADC karkashin David Mark

Shugaban INEC ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya wajabta masa bin umarnin kotu, musamman hukuncin Kotun Ƙoli, ba tare da la’akari da tasirin siyasar da hukuncin zai haifar ba.

“Idan a ƙarshe ya gaza, to, wajibi ne a gare ni ƙarƙashin Sashe na 285 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya in bi duk umarnin kotu, musamman idan daga Kotun Ƙoli ne,” in ji shi.

Sai dai Amupitan ya nuna damuwa kan yawan shari’o’in da hukumar zaɓen ke ciki, yayin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke ƙara kankama.

Ya bayyana cewa INEC na da shari’o’i sama da 300 da ke gabanta, a lokacin da saura kusan kwanaki 66 kafin zaɓen da ya yi magana a kai a baya.

Kara karanta wannan

INEC ta yi matsaya kan hukuncin kotu da ya rusa takarar Atiku a 2027

“Wasu daga cikin matsalolin da muke fuskanta sun shafi shari’o’i, akwai shari’o’i sama da 300 da ke gaban INEC, alhali saura kusan kwanaki 66 zaɓe,” in ji shi.

INEC ta bukaci a gaggauta shari’o’i

Ya bayyana cewa a baya hukumar ta goyi bayan a gaggauta sauraron shari’ar rikicin shugabancin ADC, yana mai cewa ya kamata a kammala shari’o’in da suka shafi zaɓe tun da wuri domin bai wa INEC damar tsara yadda za ta gudanar da ayyukanta.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa hukumar ta bi umarnin kotu na dakatar da matakan da take ɗauka tare da jiran sakamakon shari’ar, amma daga baya aka ɗaukaka ƙarar zuwa kotun gaba.

Amupitan ya kuma yi kira da a yi gyare-gyare domin hana shari’o’in kafin zaɓe kawo cikas ga shirye-shiryen gudanar da zaɓe.

ADC ta karbi takardar hukuncin kotu

Kun ji cewa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na ADC ya tabbatar da karɓar sahihin kwafin hukuncin kotu da ya kori shugabancin David Mark.

A makon da ya gabata, wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai Shari'a Peter Lifu ta bayar da umarnin tsige Mark daga shugabancin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262