Wani maigida ya hada baki da Likita wajen cirewa uwargidarsa mahaifa ba tare da saninta ba

Wani maigida ya hada baki da Likita wajen cirewa uwargidarsa mahaifa ba tare da saninta ba

Ana zaune kalau wani magidanci ya umurci Likita ya cirewa matarsa mahaifa don kawai ya gaji da yawan haihuwa da take yi.

Wani mutumi na neman yadda za’a shawo kan matarsa wacce ta gano ba da dadewan nan ba cewa mijinta ya hada baki da likita domin cire mata mahaifa ba tare da iliminta ba.

Wani likita mai suna Dr Harvey Olufunmilayo, ya bayyana wannan ne a shafin sada ra’ayi da zumuntarsa na Tuwita inda yake neman shawaran jama’a kan yadda zai shawo kata a jiya Laraba.

Likitan yace: “Wani abokina ya laburta min wani labarin mai ban takaici kuma suna bukatan shawaranku. Matar wani mutum na cikin bakin fushi tana ruguza ko ina saboda mijinta ya hada baki da Likita sun cire mata mahaifa ba tare da saninta ba.”

Ya kara da cewa mutumin ya dau wannan mataki ne bayan matar ta yi haihuwanta na biyar yana cewa ai bata bukatar mahifar, kuma tana son kasheshi da daukan nauyin yara.

Ya ce tun kafin yanzu ya bukaci matar su dakatad da haihuwa ta tiyata amma ta ki. Kana da kanta ta kawo shawaran cewa zata iya cire mahaifarta idan hakan zai hana haihuwa a shekarar 2015.

Yanzu dai shawara suke nema, shin idan ke ce me zakiyi?

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng