Bikin Sallah: Hotuna daga bikin hawan daushe na garin Kano

Bikin Sallah: Hotuna daga bikin hawan daushe na garin Kano

Hawan sallah dai wata al'ada ce da ta dade a tarihin masarautun kasar Hausa. Sarakunan kasar Hausa sun fara yin hawan Sallah ne bayan zubar da addinin gargajiya tare da rungumar addinin Musulunci.

A yanzu dai babu kamar masarautar Kano a kasar Hausa ta fuskar gudanar da hawan Sallah mai kayatarwa da daukan hankali.

Dubban jama'a, da suka hada da manya da yara, maza da mata har da ma baki daga fadin Najeriya da wasu kasashen, ne ke tururuwa domin kallon hawan sarkin Kano.

Bikin Sallah: Hotuna daga bikin hawan daushe na garin Kano
Hotuna daga bikin hawan daushe na garin Kano

Bikin Sallah: Hotuna daga bikin hawan daushe na garin Kano
Bikin hawan daushe na garin Kano

Bisa ga al'ada, hawan na "Daushe" shine hawa na farko da sarki a Kano ke gudanarwa a ranar sallah bayan sakkowa daga sallar idi domin gaisawa da jama'a da kuma ziyartar mahaifiyar sa (mai babban zaure) domin yin gaisuwa.

Hakimai da ragowar masu sarauta na fitowa tare da tawagarsu domin yin gaisuwa ga sarki da kuma yi masa rakiya duk inda za shi. Ana gudanar da bikin hawan ne tare da dogarai da masu busa algaita da kide-kide da wasannin gargajiya dake karawa hawan armashi.

DUBA WANNAN: Ana yiwa rayuwata barazana saboda siyasa – ‘Yar majalisa Maryam Bagel

A wannan karon, an hangi wasu gungun matasa na dauke da fastocin takarar shugaban kasa Muhammadu da na gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ma wasu 'yan siyasar.

Hawan Daushe na bana ya samu halartar mai girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da Sanata Barau I Jibril, Sanata Kabiru Gaya, Sakataren Gwamnati Malam Usman Alhaji da Dan Majalisar Jiha Baffa Babba Dan Agundi da 'yanmajalisu, kwamishinoni, shugaban jamiyyar APC Alh. Abdullahi Abbas da sauran jami'an gwamnatin Kano da sauran manyan baki daga ciki da wajan jihar Kano dama Najeriya baki daya.

Bikin Sallah: Hotuna daga bikin hawan daushe na garin Kano
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

Bikin Sallah: Hotuna daga bikin hawan daushe na garin Kano
Hotuna daga bikin hawan daushe na garin Kano

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel