Kungiyar Hakika: Kungiyoyin fafutuka sun yi a gargadi kan yawaitar yan Hakika

Kungiyar Hakika: Kungiyoyin fafutuka sun yi a gargadi kan yawaitar yan Hakika

- Wata sabuwar kungiyar ta tsiro a jihar Nasarawa

- Wannan sabuwar kungiya na lakabi da suna 'Hakika'

- Duk da suna ikirarin cewa Musulmai ne, abubuwan da sukeyi ya sabawa addinin Islama

Kungiyoyin fafutuka a jihar Nasarawa sun nuna damuwarsu kan yawaitar mambobin kungiyar Hakika a jihar da kuma yadda matasa ke shiga kungiyar.

Wani masanin harkar tsaro, Dakta Nwani Aboko, ya laburta wannan abu ne a taron da kungiyar North East Regional Initiative (NERI) ta shirya kan dakile tsatsauran ra’ayi a garin Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.

Aboki, wanda masani ne kan ilimin ta’adanci, ya bayyana cewa mutane da dama suna shiga kungiyar Hakika a garin Lafia da wasu sassan karamar hukumar Toto.

KU KARANTA: Saudiyya ta garkame Limamin Makkah da ya soki dokar halalta cakuduwan maza da mata a taruka

Ya ce wani sabon rahoto da hukumar farin hula wato State Security Services (SSS) ta saki ya bayyana cewa kungiyar na daukan dimbin matasa a Toto.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan wannan abu saboda idan bata dau mataki da wuri ba, wannan kungiya zai iya fin Boko Haram hadari ga al’umman Najeriya.

Kungiyoyin fafutukan sun kara da cewa wasu yan Boko Haram da suka tsira daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun dawo yankin Arewa maso tsakiya, Kudu maso Kudu, da kuma Kuku maso yammacin Najeriya.

Legit.ng ta kawo muku rahoto kwanakin baya kan wata rahoton da hukumar sojin kasa ta saki kan yan kungiyar hakika da ke tsiro a jihar Nasarawa.

Daga cikin akidar ya kungiyar shine ba sa Sallah da Musulmai ke yi kuma sun hallata shan giya da zinace-zinace.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel