PDP ta mutu har abada, APC kuma zata sha kashi a hannuna – Dan takarar shugaban kasa Sowore

PDP ta mutu har abada, APC kuma zata sha kashi a hannuna – Dan takarar shugaban kasa Sowore

Matashin dan takarar shugaban kasa Omoyele Sowore ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta gaza cika alkawurran da ta daukan ma yan Najeriya, don hakan yake da yakinin zai kada shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sowore yana takarar shugaban kasa ne a wata sabuwar jam’iyya mai suna ‘African Action Congress AAC’, kuma ya bayyana ma gidan talabijin na Channels cewa APC ta gaza wajen tabbatar da tsaro da inganta rayuwar mutane.

KU KARANTA: Tuna baya: idan mutum ya rasa madafa ko mai malfa ya gani sai ya bi shi – Kwankwaso

PDP ta mutu har abada, APC kuma zata sha kashi a hannuna – Dan takarar shugaban kasa Sowore
Dan takarar shugaban kasa Sowore

“APC shirme ne kawai, sun kasa cika alkawurran da suka dauka, sun yi alkawarin daukan mataki game da matsalar tsaro da ta dabaibaye kasar nan, amma har yanzu babu wani abin kirki da suka tabuka, wannan gwamnatin ta fadi, kuma wannan tabbacin zata karye kenan a 2019.” Inji shi.

Dayake tsokaci game da jam’iyyar PDP, Sowore yace ai PDP ta mutu murus, don haka babu wani tasirin da zata yi anan gaba, “idan aka hada PDP da ta mutu, da kuma APC da ta gaza, ina da tabbacin zan kai labari a 2019, zan ci zabe.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel