Daya daga cikin Kusoshin Tafiyar Obidient Ya Rabu da Peter Obi, Ya Bi ‘Dan Takara Dabam

Daya daga cikin Kusoshin Tafiyar Obidient Ya Rabu da Peter Obi, Ya Bi ‘Dan Takara Dabam

  • Jam'iyyar SDP ta naɗa tsohon shugaban ƙungiyar Obidient Movement, Yunusa Tanko, a matsayin jagoran kamfe
  • Naɗin nasa ya zo ne bayan ya yi murabus daga matsayin mai ba Peter Obi shawara kan harkokin siyasa a Arewa
  • Tanko ya yi alƙawarin haɗa kai da ɗan takarar SDP, Prince Adewale Adebayo, domin ganin an samu nasara a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Da alama Yunusa Tanko ya fice daga ƙungiyar Obidient Movement, an naɗa shi jagoran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na SDP.

Jam'iyyar SDP ta naɗa Yunusa Tanko, tsohon shugaban Obidient Movement, a matsayin jagoran kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.

Peter Obi
'Dan takaran NDC a 2023, Peter Obi da Yunusa Tanko tare da jama'a Hoto: @TheOfficialPOMA/X
Source: Twitter

Yunusa Tanko ya yi tsalle zuwa jam'iyyar SDP

The Cable ta ce an gabatar da Yunusa Tanko a matsayin sabon jagoran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar a ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Barakar cikin kungiyar dattawan Arewa ta kara munana ana saura kwanaki zabe

SDP ta gabatar da shi yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta da aka yi a Abuja.

Mark Adebayo, mai ba SDP shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa na kwamitin neman zaɓen Adebayo/Bugaje ya tabbatar da lamarin.

Da yake jawabi wurin taron, Tanko ya yi alƙawarin aiki da Adewale Adebayo, ɗan takarar shugaban ƙasan SDP, da abokin gaminsa, Usman Bugaje.

Tsohon 'dan majalisar aka jawo ya yi masa mataimaki, domin ganin sun samu nasara a zaɓen baɗi, za su tunkari Bola Tinubu da sauran 'yan takara.

Tanko ya ce SDP tana wakiltar muradun talakawa da waɗanda aka mayar saniyar ware a Najeriya.

Yunusa Tanko ya yi sallama da Peter Obi

Mista Tanko ya ce ya yi murabus daga matsayin mai ba Peter Obi shawara kan harkokin siyasa a Arewa tun a ranar 30 ga watan Oktoba 2026.

Ya bayyana cewa murabus ɗin nasa ya biyo bayan naɗa shi cikin shugabancin ƙungiyar NCFront bayan rasuwar Rt. Hon. Ghali Umar Na'Abba.

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan sanda suka garkame Farfesa Zulum saboda ya nemi tsayawa takara a Borno

A Premium Times, an rahoto cewa Mista Tanko ya ce ya tuntubi Peter Obi da Sanata Seriake Dickson kafin ya karɓi muƙamin da aka ba shi.

Sannan ya yaba masu bisa goyon bayan da suka ba shi lokacin da yake jagorantar Obidient Movement.

Ya yi alƙawarin yin aiki tare da shugabannin NCFront da Adewale Adebayo, yana mai bayanin dangantakarsa da ɗan takarar SDP tun a 2023.

Tanko ya kasance kakakin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na LP a 2023. Sanata Shehu Sani ya yi iƙirarin Obi bai da irin shi a duk Arewacin Najeriya.

A shekarar 2019, Tanko ya tsaya neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta NPC sannan ya zama shugaban ta daga baya.

Peter Obi
Peter Obi a Cross River wajen kamfen NDC Hoto: @EstherUmoh
Source: Twitter

Mutanen Peter Obi suna tafiya suna barin shi

Ana da labarin cewa ‘dan takaran NDC, Peter Obi ya yi barin mutanen shi kamar su Keneth Okonkwo, Yunus Tanko da kuma Nana Kazaure.

Na hannun daman na ‘dan siyasar sun tsallaka wajen Bola Tinubu, Atiku Abubakar da su Seyi Makinde yayin da yake harin shiga Aso Rock.

Har Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmad wanda ya yi masa abokin gami a takarar 2023 shi ma ya rabu da shi, yanzu ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar PRP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng