Mugunta ruwan fakko: Mutumin daya kashe matarsa ya gamu da fushin Kotu

Mugunta ruwan fakko: Mutumin daya kashe matarsa ya gamu da fushin Kotu

Wani magidanci da ya kashe matarsa ya boye gawar a cikin Firij ya gamu da fushin Kotu, inda ta yanke masa hukuncin kisa a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta a, inji rahoton kamfanin dillancin labaru na AFP.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kotun ta kama Zhu Xiaodong mai shekaru 31 da laifin kashe matarsa mai suna Yang Liping a shekarar 2016 bayan wata yar cacar baki data barke a tsakaninsu, sa’annan ya nannade gawar ta saka a cikin Firij.

KU KARANTA:

Abinka da mugun mutum, har tsawon watanni uku babu wanda yake da masaniya game da mutuwar Liping, shi kuwa gogannaku sai ya kwashe kudaden matar yayi ta kashe su, yana tafiye tafiye yawon bude da kasashen duniya da kuma neman matan banza.

Amma dayake alhaki dan kwikuyo ne, sai ga Zhu da kansa ya kai kansa gidan surukansa, a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar mahaifin matar tasa, inda kowa yayi tsammanin ta halarci taron, inda ya bayyana musu abinda ya faru.

Wannan lamari yayi matukar bata ma al’ummar kasar China rai, inda jama’an kasar da kansu suka bukaci a yanke ma Zhu hukuncin kisa, haka suma iyayaen Liping, sun bukaci Kotu ta yanke masa hukuncin kisa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: