Shugaba Buhari ya yi Ganawar sirri da wasu Jiga-Jigai 3 na Najeriya

Shugaba Buhari ya yi Ganawar sirri da wasu Jiga-Jigai 3 na Najeriya

A ranar Larabar da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Abia, Dakta Orji Uzor Kalu, ya jagoranci gwamnan jihar Filato Solomon Lalong da kuma Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu, zuwa wata ganawar sirri tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari gidan sa dake garin Daura.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, an gudanar da wannan ganawa bayan Sarkin Daura, Dakta Farouq Umar Farouq, ya yiwa Kalu nadin sarauta ta 'Danbaiwan Hausa yayin da tawagar ta su ta Ministan da kuma gwamnan na jihar Filato suka ziyarci fadar sa.

Bayan wannan biki na nadin sarauta, jiga-jigan uku sun nufaci gidan shugaban kasa da misalin 2.40, inda rahotanni suka bayyana cewa sun kuma yi bankwana da gidan da misalin 3:35 na yammacin ranar Larabar da ta gabata.

Sai dai Shittu yayin ganawar sa da manema labarai ya bayyana cewa, manufar ziyarar su ga shugaban kasar ba ta wuci ta ban gajiya ba sakamakon dawowa daga tafiyar sa ta neman lafiya a kasar Birtaniya.

Shugaba Buhari ya yi Ganawar sirri da wasu Jiga-Jigai 3 na Najeriya
Shugaba Buhari ya yi Ganawar sirri da wasu Jiga-Jigai 3 na Najeriya
Asali: UGC

A karshen makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya dawo kasar sa ta Najeriiya bayan hutun kwanaki goma da ya tafi zuwa Birnin Landan inda ya danka ragamar mulkin kasar nan a hannun Mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo.

A baya can Sarkin na Daura ya bayyana cewa, anyi Kalu wannan nadin sarautar ne sakamakon gudunmuwar sa marar yankewa da yake bayarwa ta hadin kan al'ummar kasar nan da kuma tsagwaran soyayyar sa ga gwamnatin shugaban kasa Buhari.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya ci gaba har bayan 2019 - Gwamna Bello

Basaraken yake cewa, Fadar sa kadai a 'kasar hausa take da ikon nadin wannan sarauta, wanda a halin yanzu ya zamto wakilin Hausa a gaba daya yankin kasar yaren Ibo a Najeriya.

A nasa jawaban, Kalu ya yabawa Sarkin dangane da wannan babbar kyauta ta nadin sarauta, tare da shan alwashi na ci gaba da bayar da gudunmuwar kawo ci gaba da hadin kai a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel