Akume Ya Dauko Abin da Ya Faru a 1999, Ya Zargi Atiku da Yunkurin Karya Alkawari a Zaben 2027

Akume Ya Dauko Abin da Ya Faru a 1999, Ya Zargi Atiku da Yunkurin Karya Alkawari a Zaben 2027

  • George Akume ya zargi Atiku Abubakar da karya yarjejeniyar karɓa-karɓar shugabancin ƙasa tsakanin Arewa da Kudu
  • Sakataren gwamnatin tarayya ya ce Arewa ba za ta nemi shugabancin ƙasa ba sai a 2031, bayan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu
  • Ya ce an bi wannan tsarin galibi a gwamnatocin da suka biyo baya, har zuwa lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya zargi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, da bijire wa yarjejeniyar karɓa-karɓa.

Sanata Akume ya ce bisa yarjejeniyar, ya kamata Arewa ta jira har zuwa shekarar 2031 kafin ta sake neman shugabancin ƙasar nan.

Akume.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume a ofishinsa a Abuja Hoto: George Akume
Source: Facebook

Vanguard ta ce ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, lokacin da yake karɓar wata tawaga daga ƙungiyar Miyetti Allah Fulaku Yesoyeso, ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa, Alhaji Abubakar Suleiman.

Kara karanta wannan

An fitar da bidiyon Seyi Tinubu yayin da ya je fadar sarkin Musulmi

Akume ya tuna tsarin karba-karba

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Yomi Odunuga, ya fitar, ya tuna cewa an cimma yarjejeniyar ne a 1999, yayin wani taron zaɓaɓɓun gwamnonin jam’iyyar PDP a Kaduna.

Ya ce marigayi Cif Solomon Lar ne ya jagoranci taron, yayin da marigayi Adamu Ciroma yake mataimakin shugaban jam’iyyar.

Yarjejeniyar ta tanadi cewa Kudu za ta yi shekara takwas a kan karagar mulkin shugaban ƙasa, sannan Arewa ta karɓi mulkin na tsawon shekara takwas.

“Na yi mamaki ganin cewa Atiku, wanda ya halarci wannan taro kuma ya amince da yarjejeniyar, yanzu yana neman shugabancin ƙasa bayan Buhari ya yi shekara takwas daga Arewa.
"Wannan ba lokacin Arewa ba ne. Arewa za ta zo takara ne a 2031,” in ji Akume.

Shin ana bin tsarin tun daga 1999?

Ya ce an bi wannan tsarin galibi a gwamnatocin da suka biyo baya, har zuwa lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki.

Kara karanta wannan

"Yadda Tinubu zai nuna wa Atiku ƙarfin siyasa, ya lashe zabe a jihohi 36 a 2027"

“Obasanjo ya yi shekara takwas, Yar’Adua ya gaje shi, amma abin takaici ya rasu. Jonathan ya karɓi mulki kuma ya yi kusan shekara shida.
"Bayan Jonathan, Buhari daga Arewa ya yi shekara takwas. Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulki daga Buhari. Ya yi shekara huɗu kacal, saboda haka saura masa shekara huɗu,” in ji shi.
Atiku Abubakar.
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar a taron kaddamar da hadaka a Abuja Hoto: @atiku
Source: Facebook

Sakataren gwamnatin tarayya ya yi gargaɗin kada wani ya kawo cikas ga yarjejeniyar saboda muradun kansa.

Akume ya ce idan shekarar 2031 ta zo, Arewa za ta kasance cikin damar fitar da duk wani ɗan takara da ta ga ya cancanta.

Atiku ya kwantar da hankalin jama'a

Kun ji cewa Atiku Abubakar ya buƙaci magoya bayansa su ci gaba da jajircewa, yana mai cewa har yanzu yana cikin tseren neman shugabancin Najeriya a 2027.

Dan takarar shugaban kasa na ADC Atiku ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen hana yunƙurin mayar da Najeriya ƙasar da jam’iyya ɗaya ce kawai ke da iko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262