Kasar Ghana ta doke Najeriya a kasar Amurka wajen kwazon aiki

Kasar Ghana ta doke Najeriya a kasar Amurka wajen kwazon aiki

- Wani sabon rahoto ya bayyana yadda aka samu koma bayan jajircewar 'yan Najeriya a kasar Amurka

- Kasashen Afrika da dama sun shiga gaban Najeriya ne bayan da Bloomberg suka wallafa rahotansu

An bayyana cewa ‘yan kasar nan da suke zaune a kasar Amurka sune na takwas a cikin jerin ‘yan kasashen waje da suke da kwazon aiki da jajircewa.

Cikin wani Rahoto da kamfanin Bloomberg ya wallafa, ya bayyana cewa Najeriya tana da maki 71, yayin da kasar Ghana ta ke da maki 75.2. Wanda hakan yake alamta cewa kasar Ghana tana da mutane wadanda suka kware tare da jajircewa a harkar aiki.

Kasar Ghana ta doke Najeriya a kasar Amurka wajen kwazon aiki
Kasar Ghana ta doke Najeriya a kasar Amurka wajen kwazon aiki

Kasar Bulgaria ce ta zo ta biyu da maki 74.2 sai kuma kasar Kenya ta ke biye mata da kaso 73.4 inda ta zama a mataki na uku.

Sauran su ne kasar Ethiopia a matsayi na hudu, sai kuma kasar Egypt a matsayi na biyar da kuma kasar Liberia wacce ta ke a matsayi na tara.

Wannan ya zama wata manuniya dake nuni da cewa lallai 'yan ciranin da suka fito daga nahiyar Afrika zuwa kasar Amurka suna da kwazo da nagartar aiki, fiye da wadanda suka fito daga kasar Mexico da kuma nahiyar Amurka ta tsakiya, wadanda su ne kaso 70 cikin dari na ‘yan ciranin da suke zaune a kasar ta Amurka.

KU KARANTA: Hankalinmu ya karkata ne wajen fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo

Tun da farko dai kamfanin Bloomberg yayi amfani da wani rahoto hukumar kidaya ta kasar Amurka ta gudanar a shekarar 2016 kan ‘yan ciranin da suke cikin kasar ta. Wanda rahoton ya bayyana kasar Najeriya a matsayi na 8 a cikin ‘yan cirani masu Ilimi da suke zaune a kasar ta Amurka.

Kasar Ghana ta doke Najeriya a kasar Amurka wajen kwazon aiki
Kasar Ghana ta doke Najeriya a kasar Amurka wajen kwazon aiki

Rahoton ya kara da cewa ‘yan Najeriya da suka shiga cirani kasar Amurka bisa doka da oda sun kai kimanin 262,603.

Kasashen Kenya da Nijeriya da Nepal da kuma kasar Ghana su ne kasashen da suka fi yawan al'ummar da suke neman Ilimin gaba da Sakandire a kasar ta Amurka. Sannan kuma suna kusa da kunnen doki a yawan ma'aikata da yawan adadin masu neman Ilimi.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel