Mahajjacin Najeriya ya mayar da kudi N485,000 da ya tsinta cikin bayi a Makkah

Mahajjacin Najeriya ya mayar da kudi N485,000 da ya tsinta cikin bayi a Makkah

- Wani Alhajin Najeriya ya misalta hali na kwarai a Saudiyya

- Ya mayar da wasu makudan kudi da ya tsinta a jiya

Wani mahajjacin Najeriya mai suna Musa Muhammad Edotsu ya samu ladan $200 a matsayin tukuici bayan ya mayar da kudin da ya tsinta cikin bayi a Muna ranan Laraba, 22 ga watan Agusta 2018.

Kudaden da ya tsinta ya kunchi $1,200 (N435,180), Riyal 492 (N47,586) da dirhami 65.

Mahajjacin wanda dan karamar hukumar Gbago na jihar Neja ya tsinci jakan ne dauke fasfot, mukulli, da kudade.

Ba tare da bata lokaci ba, Musa ya ya kaiwa hukumar mahajatan jihar Neja da suka nemo mammalakin jakan.

Mahajjacin Najeriya ya mayar da kudi N485,000 da ya tsinta cikin bayi a Makkah
Mahajjacin Najeriya ya mayar da kudi N485,000 da ya tsinta cikin bayi a Makkah

Amirul Hajj na jihar Neja, Alhaji Abubakar Magaji, ya mika kudin ga asalin mammalin kudi, Alhaji Zulkalnain Sa’eed, wanda shine shugaban hukumar mahajjatan jihar Enugu.

Abubakar Magaji ya yabawa wannan hali na kwarai a lokacin da wani kudaden wasu mahajjata ya fara karewa.

KU KARANTA: Wani maigida ya hada baki da Likita wajen cirewa uwargidarsa mahaifa ba tare da saninta ba

Ya ce hukumar hajjin jihar Neja za ta baiwa Edotsu kyautan $200 bisa wannan abin azo a gani da yayi.

Mammalakin kudin Alhaji Sa’eed ya nuna farin cikinsa kuma ya yi godiya ga Edotsu kan wannan halin gaskiya da ya nuna da dawo da kudin.

Yayi kira ga sauran mahajjatan Najeriya da suyi koyi da irin wannan hali na kwarai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel