Zangon mulki falle daya mai shekaru 6 ne yafi dacewa da kasar nan – Maitaimakin Bukola Saraki

Zangon mulki falle daya mai shekaru 6 ne yafi dacewa da kasar nan – Maitaimakin Bukola Saraki

- Batun sauyin fasalin kundin tsarin mulkin kasar nan ya sake kunno kai

- Wani Sanata ya yi kira da soke tsarin tazarce ga shugaban kasa da gwamnoni

A jiya ne mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu ya kara nanata kiran da yake yi akan zangon mulki daya mai shekaru 6 kan karagar mulkin kasar nan, tsakanin gwamnoni da shugaban kasa.

Zangon mulki falle daya mai shekaru 6 ne yafi dacewa da kasar nan – Maitaimakin Bukola Saraki
Zangon mulki falle daya mai shekaru 6 ne yafi dacewa da kasar nan – Maitaimakin Bukola Saraki

“Idan aka yi haka zai rage hayaniyar siyasa da kuma hana dabi'ar nan da masu mulki suke yi ta gadar kawunansu".

Sanata Ekweremdun ya bayyana hakan ne a shafinsa na kafar sadarwa ta facebook.

Ya kara da cewa “Kusan a kowanne lokaci lamarin yana zama wani abun magana musamman a duk lokacin da aka fara kada gangar siyasa".

“Abin gwanin ban takaici, domin kuwa hadarin siyasa a kasar nan yayi gangankon da yake hade da rigingimu irin na siyasa, wanda har sai ya kai matakin zaben shekarar 2019".

KU KARANTA: Aiyuka 4 da Buhari bai taba sanya mana baki ciki ba - Fashola

”Daga yadda yanayin siyasar kasar nan ya dumama, hakan zai gaskata abin da wasu daga cikinmu muke kira akan a mayar da zangon mulki falle daya mai tsahon shekaru shida ga gwamnoni da shugaba kasa".

Sanata Ekwemeradu ya kuma bayyana cewa duk da al'ummar kasar nan sun fi sabawa da mulkin zango biyu mai shekaru 4, amma kuma komai yana canzawa domin kuwa al'ummar ta canza, wanda hakan zai bayar da dama wajen yiwa kundin tsarin mulkin kasar nan kwaskwarima.

”Mun yi kokarin gabatar da zangon mulki falle daya a lokacin da ake aikin yiwa kundin tsarin mulkin kasar nan gyaran fuska, a zauren majalisar kasar nan, amma abin takaici, sai jam’iyyun siyasa da kungiyoyin suka kasa fahimtar mu bisa wasu dalilansu. Wanda hakan ya sanya lamarin bai kai ga nasara ba". Sanatan ya bayyana takaicinsa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel