Kwana 2 kafin Ziyarar Tinubu, Yan Bindiga Sun Kewaye Gari Sun Bude Wa Mutane Wuta
- ’Yan bindiga sun kai hari kauyen Mista Ali da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da mutum biyar tare da harbin wasu mutum biyu da suka jikkata
- Sarkin gargajiyar yankin ya bukaci gwamnati da jami’an tsaro su gaggauta ceto wadanda aka sace cikin koshin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum biyar tare da harbin wasu mutum biyu a yayin wani hari da suka kai al’ummar Mista Ali da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato.
Yan ta'addan dauke da makamai sun mamaye yankin ne a daren ranar Alhamis, inda suka bude wuta, lamarin da mazauna yankin suka ce ya jefa al’ummar cikin firgici.

Kara karanta wannan
Mataimakin shugaban majalisa ya ga ta kansa da ya yi ƙokarin tallata Tinubu a taron jama'a

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mazauna yankin sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya kudin fansa, amma iyalan wadanda aka sace ba su biya ba tukuna.
Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Sarkin gargajiya na Mista Ali, Danladi Akinja Kasuwa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce harin ya zo wa mazauna yankin ba zato ba tsammani.
Ya ce:
"Mun dai ji karar harbe-harbe daga ko'ina a yankin. Maharan sun mamaye garin a lokacin, suka fara harbe-harbe babu kakkautawa, lamarin da ya sa mutane suka rika gudun neman mafaka."
Danladi ya ce an sace mutum biyar a yayin harin, yayin da wasu mutum biyu suka samu raunukan harbin bindiga, kuma aka garzaya da su asibiti domin yi musu magani.
Halin da mutane suka shiga
Da yake nuna damuwarsa kan lamarin, basaraken ya ce:
"Muna cikin damuwa matuka kan abin da ya faru a al'ummarmu. Muna rokon gwamnati da jami'an tsaro su kara karfafa tsaro a yankin domin hana sake samun irin wadannan hare-hare."
Bugu da kari, basarken ya bayyana harin a matsayin abin tayar da hankali, yana mai cewa lamarin ya haifar da fargaba da rashin tabbas a tsakanin mazauna yankin.
Basarake ya aika sako ga gwamnati
Ya kuma nuna damuwa kan lafiyar mazauna yankin, tare da kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar mataki, kamar yadda Leadership ta rahoto.
"Muna son jami'an tsaro su kara kaimi wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata wannan hari," in ji shi.

Source: Original
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato, SP Alabo Alfred, bai mayar da martani kan tambayar da wakilinmu ya aika masa ba.
Wannna na zuwa ne kwana biyu kafin ziyarar da aka tsara Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ji jihar Plateau domin halartar kamfe ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026.
Yan bindiga sun kashe mutum 3
Kun ji cewa yan bindiga sun kashe mutane uku da wani jami'in tsaro yayin wani hari da suka kai ƙauyen Bel da ke yankin Sho, a ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Plateau.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00na daren Lahadi, 8 ga watan Nuwamban 2026 lokacin da maharan suka kutsa cikin ƙauyen tare da buɗe wa mazauna yankin wuta.
Asali: Legit.ng
