Wani mutum ya fara tattaki daga Legas zuwa Abuja don nuna rashin amincewa da takarar Buhari

Wani mutum ya fara tattaki daga Legas zuwa Abuja don nuna rashin amincewa da takarar Buhari

- Bayan Suleiman Hashimu da Duduwale, wani matashi ya fara tattaki

- Zai yi tattakin daga jihar Legas zuwa Abuja

- Amma a wannan karon, don juyawa Buhari baya

Wani mutumi mai suna Isa Mohammed Munlaila, ya fara tattaki daga jihar Legas zuwa birnin Abuja domin nuna rashin amincewarsa da sake takarar shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2019.

Munlaila, wanda yayi magana da manema labarai a ranan Alhamis a jihar Legas ya ce ran matasa ya baci kan Buhari saboda gazawarsa na tsawon shekaru uku da yah au mulki yanzu.

Ya kara da cewa mutane na cikin halin ha’ula’I, tsadar rayuwa ya karu kuma shugaban kasa ya saba alkawuransa da ya yiwa yan Najeriya a shekarar 2015.

Munaila yana dauke da karamar akwati mai launin tutan Najeriya sannan ya rike makara mai rubutu “ R.I.P APC” wato APC ta mutu.

KU KARANTA: Sabuwar rikici ta barke a jam'iyyar PDP a wata jihar Arewa

Za ku tuna cewa matashi Suleiman Hashimu ya yi irin wannan tattaki daga Legas zuwa Abuja domin murnan nasarar Buhari a 2015.

Wani mutum ya fara tattaki daga Legas zuwa Abuja don nuna rashin amincewa da takarar Buhari
Wani mutum ya fara tattaki daga Legas zuwa Abuja don nuna rashin amincewa da takarar Buhari

Hakazalika Abubakar Duduwale ya yi tattaki daga birnin Yola zuwa Abuja. Kwanan nan, Duduwale ya fara samun ciwon kafa wanda ya kwantar da isa a asibiti. Amma ba tare da bata lokaci ba, gwamnatin shugaba Buhari ta tura ministan kiwon lafiya domin dubasa a garin Yola.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel