Abubuwan da Suke Nuna Lokacin Tashin Kiyama Ya Yi a Musulunci

Abubuwan da Suke Nuna Lokacin Tashin Kiyama Ya Yi a Musulunci

  • Bayanan Sheikh Muhammad bin Salih Al-Munajjid sun nuna cewa babu wani ingantaccen dalili da ya tabbatar da cewa Alƙiyama za ta tashi a shekarar 2026
  • Malamin ya ce alamomin tashin Alƙiyama sun kasu gida biyu, kanana da manya, kuma wasu daga cikin kananan alamomin sun riga sun bayyana
  • Ya bayyana cewa manyan alamomi guda 10 ne za su bayyana a kusa da tashin Alƙiyama, kuma za su biyo juna cikin dan kankanin lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Sheikh Muhammad bin Salih Al-Munajjid ya yi karin bayani kan alamomin tashin Alƙiyama, musamman bayan wasu mutane sun nuna rudani kan rade-radin cewa za a yi tashin Alƙiyama a shekarar 2026.

A cikin bayaninsa, malamin ya bayyana cewa alamomin tashin Alƙiyama su ne abubuwan da za su faru kafin tashinta, wadanda za su nuna kusantowar wannan babbar rana.

Kara karanta wannan

An yi arangama da 'yan daba suka kai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso

Taswirar duniya
Taswirar duniya dauke da kasashe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A sakon da ya wallafa a shafinsa, ya ce malamai sun raba alamomin zuwa kanana da manya, inda wasu daga cikin kananan alamomin suka riga suka faru.

Alamomin tashin Alƙiyama kanana

Sheikh Al-Munajjid ya bayyana cewa kananan alamomin tashin Alƙiyama suna da yawa, kuma an ambace su a cikin hadisai ingantattu.

Daga cikin wadannan alamomi akwai:

  1. Aiko Annabi Muhammad (SAW).
  2. Rasuwar Annabi Muhammad (SAW).
  3. Bude birnin Kudus.
  4. Barkewar annobar Amwas a Falasdinu.
  5. Yawaitar dukiya har mutane su daina bukatar karbar sadaka.
  6. Yawaitar fitintinu, kamar kisan Halifa Usman bn Affan, yakin Jamal da Siffin, bayyanar Khawarij da yakin Harra.
  7. Bayyanar masu ikirarin annabci, kamar Musailama makaryaci da Al-Aswad Al-Ansi.
  8. Bayyanar wata babbar gobara a yankin Hijaz a shekarar 654 bayan hijira.
  9. Rashin amana, inda ake dora al’amuran jama’a a hannun mutanen da ba su cancanta ba.
  10. Raguwa da gushewar ilimi sakamakon rasuwar malamai, tare da yawaitar jahilci.
  11. Yawaitar zina.
  12. Yawaitar cin riba.
  13. Yawaitar amfani da kayan kida.
  14. Yawaitar shan giya.
  15. Makiyaya za su rika gogayya wajen gina dogayen gine-gine.
  16. Yaro zai rika mu’amala da mahaifiyarsa kamar yadda maigida ke mu’amala da baiwarsa, ta hanyar wulakanci da rashin biyayya.
  17. Yawaitar kisan kai.
  18. Yawaitar girgizar kasa.
  19. Bayyanar rushewar kasa, sauyin halitta da duwatsun da za su sauko daga sama.
  20. Bayyanar matan da suke sanye da tufafi amma kamar ba su sanya komai ba.
  21. Mafarkan muminai za su rika tabbata.
  22. Yawaitar shaidar zur da boye gaskiyar shaida.
  23. Yawaitar mata fiye da maza.
  24. Kasashen Larabawa za su koma da ciyayi da koguna.
  25. Kogin Furat zai bankado wani dutse na zinariya.
  26. Dabbobin daji da wasu abubuwa marasa rai za su rika magana da mutane.
  27. Yawaitar Rumawa da kuma yakinsu da Musulmi.
  28. Bude birnin Konstantinoful.

Kara karanta wannan

Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

Malamin ya bayyana cewa wadannan alamomi ba duka za su faru a lokaci guda ba, domin wasu sun riga sun faru, wasu kuma suna ci gaba da bayyana.

Manyan alamomin tashin Alƙiyama10

Sheikh Al-Munajjid ya bayyana cewa manyan alamomin tashin Alƙiyama guda 10 ne, kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana a hadisin Huzaifa bn Usaid Al-Gifari.

Ga jerin manyan alamomin:

  1. Bayyanar Dujal.
  2. Saukar Annabi Isa bn Maryam (AS).
  3. Bayyanar Ya’juj da Ma’juj.
  4. Rushewar kasa a gabashin duniya.
  5. Rushewar kasa a yammacin duniya.
  6. Rushewar kasa a yankin Larabawa.
  7. Bayyanar hayaki mai rufe duniya.
  8. Fitowar rana daga yammacin da take faduwa.
  9. Bayyanar dabbar kasa wadda za ta yi magana da mutane.
  10. Bayyanar wuta daga Yemen wadda za ta kori mutane zuwa wurin taruwarsu.
Muhammad Salih Al-Munajjid
Sheikh Muhammad Salih Al-Munajjid. Hoto: Muhammad Salih Al-Munajjid
Source: Facebook

Malamin ya ce wadannan manyan alamomi za su bayyana ne daya bayan daya, kuma da zarar ta farko ta bayyana, sauran za su biyo bayanta cikin dan kankanin lokaci..

Hasashen tashin duniya a 2026

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani bincike ya yi hasashen cewa yawan al’ummar duniya zai kusan kai wani matsayi da ba shi da iyaka a ranar 13 ga Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisa ya ga ta kansa da ya yi ƙokarin tallata Tinubu a taron jama'a

Masu binciken sun yi gargadin cewa matsalar ba za ta kasance yunwa kadai ba, domin yawan jama’a zai iya kaiwa matakin da mutane za su fara rasa isasshen sararin zama da gudanar da rayuwarsu.

Sai dai hasashen bai cika tafiya yadda aka tsara ba, saboda yawan haihuwa a duniya ya ragu sosai tun daga shekarar 1960 kuma babu alamun hasashen zai faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng