Korafi Ya Kare, INEC Ta Bullo da Sabon Tsari kan Tura Sakamakon Zabe zuwa IReV a 2027
- INEC ta bullo da sababbin matakan fasaha domin dakile tura sakamakon zaɓe mara inganci da aringizon ƙuri’u a shafinta na IReV
- Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya ce za a hana sakamakon da bai dace ba shiga shafin kafin jama’a su gan shi
- INEC za ta gudanar da gwajin amfani da na’urorin tantance masu zaɓe da kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙasar ranar 28 ga Nuwamba, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
London - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ƙaddamar da sababbin matakan fasaha da za su taimaka wajen tsaftace tattara sakamakon zabe a shafinta na intanet watau IReV.
INEC ta ce stakan za su hana sakamakon zaɓe mara inganci da alkaluman da ke nuna an kaɗa ƙuri’u fiye da yawan masu zaɓe a mazaba bayyana a shafinta na nuna sakamako (IReV).

Kara karanta wannan
Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027

Source: Facebook
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Landan na kasar Birtaniya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
INEC ta samar da kariyar fasaha
Ya ce hukumar INEC ta gano wasu kura-kurai a tsarin tattaara sakamakon zaɓe bayan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Adedayo Oketola, ya fitar, Amupitan ya ce sababbin matakan kariya za su tabbatar da gano sakamakon da bai dace ba tare da hana shi shiga shafin da jama’a ke gani.
“Yanzu mun samar da wani matakin kariya na fasaha: idan sakamako bai inganta ba a rumfar zaɓe, ba zai shiga IReV kwata-kwata ba,” in ji shi.
Shugaban INEC ya bayyana hakan ne a wajen wani taron tattaunawa na manyan jami’ai a Chatham House, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar Kimpact Development Initiative (KDI) a Landan.
INEC ga gano kuskure a zaben 2023
Ya bayyana cewa binciken da INEC ta gudanar bayan zaɓen 2023 ya gano cewa cibiyoyin tattara sakamako na daga cikin manyan wuraren da ake samun matsaloli wajen tafiyar da sakamakon zaɓe da sanar da shi.
“Mun gano cewa babbar matsalar tafiyar da sakamakon zaɓe da sanar da shi a Najeriya ba ta rumfunan zaɓe take ba, tana cibiyoyin tattara sakamako ne,” in ji shi.
Amupitan ya ƙara da cewa hukumar na aiki don kawar da bambance-bambancen da ke tsakanin alkaluman da aka samu a rumfunan zaɓe da bayanan da ke cibiyoyin tattara sakamako, domin ƙara inganta sahihancin tsarin zaɓe.
INEC za ta yi gwajin zaɓe
Ya kuma sanar da cewa INEC za ta gudanar da gwajin tantance masu zaɓe da kaɗa ƙuri’a a duk faɗin ƙasar ranar 28 ga Nuwamba, 2026, domin gwada shirye-shiryen fasaharta na zaɓen 2027.
Amupitan ya ce hukumar ta yi la’akari da amfani da wata sabuwar fasahar zaɓe gaba ɗaya a zaɓen 2027, amma ta yanke shawarar inganta na’urorin da take da su saboda ƙarancin lokacin da ya rage kafin zaɓen.
INEC za ta bi umarnin kotu
Kun ji cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan halascin takarar Atiku Abubakar a 2027.
Amupitan ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya wajabta masa bin umarnin kotu, musamman hukuncin Kotun Ƙoli, ba tare da la’akari da tasirin siyasar da hukuncin zai haifar ba.
Asali: Legit.ng
