Aminu Ibrahim
8421 articles published since 21 Agu 2017
8421 articles published since 21 Agu 2017
A yau Asabar ne yarimomin Saudiyya sun gudunar da wata zanga-zanga a fadar Sarkin kasar na Riyadh saboda dakatar da biyan kudin ruwa da wuta da gwamnatin kasar ta saba biya musu tun fil azan. Hakan ya faru ne saboda canji.
Babban manajan kamfanin kula da kasuwar Babban Birnin Taraya Abuja, (AMML) kuma tsohon surukin Sanata Goje, Abubakar Faruk ya shigar da kara a kotu inda ya ke bukatar kotun ta tabbatar masa da cikakiyar ikon renon yar ta su.
Wata kungiya mai zaman kanta, Global Peace and Life Initiative (GOPRI) ta nuna bacin ranta bisa kalaman Sifeta Janar na rundunar yan Sandan Najeria, Ibrahim Idris da ya ce harin da aka kai a Benue bashi da alaka da Fulani Makiyaya
Gobara ta cinye wata gonan rake mai fadin hecta 30 a kauyen Mai-Ramu da ke karamar hukumar Koko/Besse da ke jihar Kebbi. Shugaban karamar hukumar, Alhaji Shu'aibu Ibrahim ne ya bayyana wa kamfanin dillanci labarai a ranar Juma'a.
Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya yi kira ga malaman addinin musulunci su rika amfani da wa'azin su wajen wanzar da zaman lafiya ke kyautata halayen al'umma kamar yadda yake cikin addinin muslunci..
Gwamnatin jihar Kwara ta yi karin girma ga malaman makarantu guda 13,931 karin girma a kananan hukumomi 16 da ke jihar. Ciyaman na hukumar bayar da ilimin firamare (SUBEB), Alhaji Jimoh Lambe ne ya bayyana hakan ranar Juma'a.
Farashin shinkafar gida Najeriya a kasuwani ya ragu da 25%, hakan ya faru ne bayan girbe amfani gona da manoman shinkafa su ka yi cikin yan kwanakin nan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito.
Labari ya zo mana daga jaridar Punch cewar dan sandan farin kaya (CIB), da ke yi wa matar Gwamnan Jihar Taraba, Anna Darius Ishaku hidima, ya rasa ransa yayin da motar sa wacce ke cikin tawagar Gwamnan, ta yi hatsari.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen kasa a jihar Kaduna. Ana sa ran karin jiragen sau saukaka zirga-zirga musammaman ga ma'aikatan jihar Kaduna masu aiki a garin na Abuja. Jiragen za su sawake sufuri ga al'umma.
Aminu Ibrahim
Samu kari