An kama Yarimomin Saudiyya bisa zanga-zanga
- An kama wasu yarimomin Saudiyya bisa laifin gudanar da zanga-zanga a fadar Sarkin na Saudiyya
- Yarimomin sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin amincewar su da sabuwar dokar da ta janye kudaden wuta da ruwa da gwamnati ke biya musu a baya
- An kama su an kule a gidan yarin al-Hayer bayan sun ki bin umurnin dakatar da zanga-zangar
A yau Asabar ne yarimomin Saudiyya sun gudunar da wata zanga-zanga a fadar Sarkin kasar na Riyadh saboda dakatar da biyan kudin ruwa da wuta da gwamnatin kasar ta saba biya musu tun fil azan.
Kafar yada labarai na sabq.org ta ruwaito cewa yarimomin sun taru ne a Qasr a-Hokm, wani fili mai dimbin tarihi a fadar sarautar ta Saudiyya inda suka bukaci a dakatar da dokar ta janye biya musu kudin ruwa da wutar lantarki.
DUBA WANNAN: Ana rigima a cikin gidan Sanata Danjuma Goje
Sun kuma bukaci a biya su diyyar kisa da aka yi wa wani dan uwan su sai dai an sanar da su cewa abin da suke bukata ba zai yiwu ba amma suka ki barin fadar, hakan yasa aka bawa yan sandan fadar izinin kama su da tsare su a gidan wakafi na al-Hayer kana daga baya a gabatar da su gabar kuliya
Jaridar ba ta bayana sunayen yarimomin ba amma ta ce jagoran su ana yi masa lakani da S.A.S. Jaridar ta kara da cewa shari'ah bata banbanta wa tsakanin al'umma kuma duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci da doka ta tanada.
A shekarar da ta gabata ne kasar na Saudiyya ta fara wasu sauye-sauye wanda suka hada ta cire tallafi da kuma bulo da sabbin haraji na kayan masarufi da kuma janye wasu kudade da ake biya ga iyalan gidan saurautar kasar. An fara gudanar da sauye-sauyen ne saboda fadin farashin kudin man fetur a kasuwa duniya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng