Gwamnatin jihar Kwara ta yi wa malaman makaranta 13,931 karin girma
- Malaman makaranta a jihar Kwara sun shiga sabuwar shekara da kafar dama
- Hakan kuwa ya faru ne bayan gwamnatin jihar ta yi karin girma ga malamai 13,931 daga kananan hukumomi 16 da ke jihar
- Ciyaman na hukumar ilimin firamare a jihar ya yi fatan karin girman zai sa malaman su kara gwazo wajen gudanar da ayyukan su
Gwamnatin jihar Kwara ta yi karin girma ga malaman makarantu guda 13,931 karin girma a kananan hukumomi 16 da ke jihar. Ciyaman na hukumar bayar da ilimin firamare (SUBEB), Alhaji Jimoh Lambe ne ya bayyana hakan ranar Juma'a yayin da yake mika masu takardun karin girman.
Bayan ya kammala bayar da takardun karin girman ga Sakatarorin ilimi na kananan hukumomin, Lambe ya mika godiyar sa ga gwamnan jihar ta Kwara bisa amincewa da karin girmar da akayi wa malaman.
DUBA WANNAN: Labari mai dadi: Farashin shinkafa ya ragu da 25% a Maiduguri
A cewarsa, sun cancanci karin girmar kuma yana fatan hakan zai faranta wa malaman rai bugu da kari zai sa su kara gwazo wajen gudanar da ayyukan su. Ya kuma kara jadada niyyar gwamnatin jihar wajen habbaka fanin ilimi musamman na firamare duk da halin karancin kudi da ake fama da shi.
A jawabin godiya da yayi a madadin sauran Sakatarorin ilimi a jihar, Sakataren karamar hukumar Ekiti, Mista Felix Olusola ya mika godiyar su ga gwamnan jihar, ya ce karin girmar tambar tukwici ne na sabuwar shekara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng