Dubi jihohin da suka yi zarra wajen cin jarrabawar NECO a bana

Dubi jihohin da suka yi zarra wajen cin jarrabawar NECO a bana

- Jihar Zamfara ne ta fi kowacce jiha fadi jarrabawar yayin da jihar Ogun ne kan gaba wajen cin jarabawar

- Sakamakon da aka fitar kwanaki 38 bayan rubuta jarrabawar ya nuna cewa jihar Filato ne kan gaba wajen magudin jarrabawa

- Abuja da Jihohin Kogi, Ondo da Taraba sun fi kowace Jiha kamewa ga barin satar amsa

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar dalibai na SSCE da aka rubuta cikin watan Nuwamba/Disambar 2017. Cikin dalibai 42,429 da su ka zauna rubuta jarabawar, 32,912 sun samu kiredit 5 ko fiye da hakan.

A hirar da jaridar New Telegraph tayi da Shugaban Hukumar, Farfesa Charles Uwakwe, ya bayyana cewan sakamakon ya fito ne bayan kwanakin da ba su wuce 38 da rubuta jarrabawar ba.

Dubi jihohin da sukafi zara wajen cin jarabawar NECO
Dubi jihohin da sukafi zara wajen cin jarabawar NECO

Legit.ng ta samu tattaro maku bayanai na yadda Jihar Ogun ta fi kowace Jiha cin jarrabawar, a inda mutane 4,766 cikin 5,213 su ka ci kiredit 5 ko fiye da hakan. Jihar Zamfara kuwa ta fi kowace Jiha samun sakamako mafi muni, a inda cikin mutane 186, mutane 24 kacal su ka ci jarrabawar.

Ita kuwa Jihar Filato, ta fi ko wacce Jiha yin satan amsa a jarabawar. Sai kuma birnin Tarayya Abuja da Jihohin Kogi da Ondo da Taraba sun fi ko ina kamewa ga barin satar amsa.

Uwakwe ya shawarci wadanda su ka rubuta jarrabawar da su duba sakamakon su a shafin Hukumar na yanar gizo, www.mynecoexam.com, ba da jimawa ba ita kuma Legit.ng ta kawo maku rahoton cewa Hukumar ta NECO ta gama ginin ta na naira miliyan 120, wanda ta yi shekaru 10 ta na yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164