Harin Benue: Kungiya ta cacaki Sifeta Idris, ta bukaci a sallame shi daga aiki
- Kungiyar ta bukaci hakan ne bisa kallaman da ya furta na cewa hare-haren Benue rikicin ne tsakanin unguwani duk da cewa mutanen garin sunyi ikirarin Fulani makiyaya ne
- Kungiyar ta ce abin kunya ne babban jami'in dan sanda kaman Sifeto Janar ya furta irin wannan maganar ba tare da ya jira sakamakon bincike ba
- Kungiyar ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya gagauta sallamar Sifeta Janar din kafin ya sake tafka wani abin kunyar
Wata kungiya mai zaman kanta, Global Peace and Life Initiative (GOPRI) ta nuna bacin ranta bisa kalaman Sifeta Janar na rundunar yan Sandan Najeriya, Ibrahim Idris da ya ce harin da aka kai a Benue bashi da alaka da Fulani Makiyaya ila iyaka rikici ne tsakanin garuruwa. Kungiyar ta ce kalaman nasa ba komai bane ila ganganci, rashin sanin makamashin aiki da yunkurin kauda hankalin al'umma.
Babban directan Kungiyar, Mista Melvin Ejeh ne ya bayyana hakan a garin Jos a yayin da yake jawabi ga hadadun kungiyoyin matasa daga jihohin arewa ta tsakiya.
DUBA WANNAN: Sojoji sun yiwa shugaban kungiyar Boko Haram babban lahani
Kungiyar ta kara da cewa abin kunya ne irin wannan kalaman su rika fitowa daga bakin jami'in wanzar da tsaro na farko ga shugaban kasa mafi girma a Africa, Kungiyar ta yi kira ga shigaba Muhammadu Buhari ya sallame Sifeta Janar din daga aiki kafin ya sake kunyata Najeriya.
Ejike ya ce ba daidai bane jami'in dan sanda mai babban matsayi kamar Sifeta Janar din ya kada baki ya fadi wannan maganar ba tare da ya jira an gudanar da sahihiyar bincike ba.
Ya ce kallamun da suka fito daga bakin Sifeta Janar din na nuna cewa ba za'a yi adalci cikin binciken tunda har ya kada baki ya fada hakan kafin yin bincike. Ya kara da cewa irin wannan kalaman na iya haifar da fitina a kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng