Matashi ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga a Katsina
- Wani matashi ya mutu nan take bayan an harbe shi a kirji
- Matashin ya bada umurnin a harbe shi ne bayan mai maganain ya bashi tabacin harsashi ba za ta ratsa jikin sa ba
- Jami'an tsaro sunyi ram da mai bada magananin kuma za'a gurfanar dashi gaban kotu a watan Febrairun 2018
Hukuma ta damke wani mai sayar da maganin gargajiya, Usman Saidu, bisa laifin salwantar da rayuwar wani matashi dan shekara 27 mai suna Aliyu Yahuza a jihar Katsina.
An gano cewa marigayin ya mutu ne bayan ya saya maganin bindiga daga hannun Usman Saidu wanda ya tabbatar masa cewa babu wani harsashi da zai iya ratsa jikin sa idan ya sha.
KU KARANTA: Ba za mu biya albashi ga malaman da ke yajin aiki ba - Gwamna El-Rufa'i
Domin gwada ingancin maganin, Yahuza ya bayar da umurnin a harbe shi a kirji da bindigar farauta sai dai harsashin ya ratsa shi kuma hakan yayi sanadiyar mutuwar sa nan take.
Hakan yasa hukuma ke tuhumar Saidu da laifin cin amana da kisan kai. Mai maganin gargajiyar mai shekaru 42 a duniya zai cigaba da zama a tsare har zuwa ranar 22 ga watan Febrairu inda babban Majistare Hajiya Fadila Dikko za ta saurara karar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng