'Ƙwarewar da Ɗana ke da Ita na Zama Gwamna': Sule Lamido Ya Magantu
- Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce dansa Mustafa Lamido na da ilimi, basira da cancantar zama gwamnan jihar
- Sule Lamido ya bukaci masu sukar takarar dansa da su tantance kwarewarsa da kansa, maimakon alakanta burinsa da tasirin mahaifinsa
- Ya bayyana cewa Mustafa na da digirin digirgir (PhD) a fannin kimiyyar siyasa, kuma ya kamata a ba shi damar gabatar da cancantarsa ga al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Sule Lamido, ya kare burin dansa, Mustafa Lamido, na neman kujerar gwamnan jihar a zaben 2027, yana mai cewa yana da dukkan cancantar rike mukamin.
Sule Lamido ya ce dansa na da ilimi, basira da kwarewar da ake bukata domin jagorantar jihar, don haka bai kamata a rika kallon burinsa ta fuskar tasirin siyasar mahaifinsa ba.

Source: Facebook
Sule Lamido ya magantu kan kwarewar ɗansa
Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na ARISE News ranar Alhamis, inda ya yi magana kan zaben 2027, jam'iyyar PDP da kuma siyasar Jigawa.
Da yake kare takarar dansa, Lamido ya ce Mustafa na da cikakkiyar basira da cancantar tsayawa takarar gwamna.
Ya ce:
"Na yi imanin Mustafa yana da basira, ilimi da cancantar gabatar da kansa ga jama'a."
A watan Mayun 2026, Mustafa ya shiga takarar gwamnan Jigawa a hukumance bayan ya karbi fom din tsayawa takara a karkashin jam'iyyar PDP.

Source: Facebook
Zurfin ilimi da dan Sule Lamido ke da shi
Mahaifinsa ya kuma bayyana cewa dansa yana da digirin digirgir (PhD) a fannin kimiyyar siyasa, inda ya bukaci masu shakkar cancantarsa da su tuntube shi domin tantance kwarewarsa.
Tsohon gwamnan ya kalubalanci masu sukar dansa da su duba iya jagorancinsa da abin da zai iya cimmawa, maimakon dogaro da goyon bayan da mahaifinsa ke masa.
Ya ce:
"Ku tuntube shi. Ku gano ko yana da basira ko babu. Ko zai iya kawo ci gaba ko ba zai iya ba. Ku yanke hukunci da kanku."
Lamido ya kara da cewa ya kamata a dauki dansa a matsayin mutum mai nasa ra'ayin siyasa da burinsa, duk da kasancewarsu uba da da cewar Punch.
Ya jaddada cewa kasancewarsu uba da da ba yana nufin dole ne ya rika magana a madadin dansa ba, domin kowannensu na da nasa halayya da manufofi.
Sule Lamido ya magantu kan takarar Obi, Atiku
A wani labarin, an ji cewa tsohon gwamna a jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce rashin hadin kan Atiku Abubakar da Peter Obi yana kara wa Shugaba Bola Tinubu damar lashe zaben 202.
Lamido ya bayyana cewa da Atiku da Obi sun hada kai, da za su fi samun karfin kalubalantar Tinubu, inda ya ba da shawarar cewa Atiku ya zama dan takarar shugaban kasa.
Ya kuma yi gargadin cewa ko wane daga cikin manyan 'yan takarar ya lashe zaben, Najeriya ba ta da riba idan aka ci gaba da fifita burin siyasa kan hadin kan kasa.
Asali: Legit.ng

