Wanda ya fara bankado zargin alakar Dan Bello da Seyi Tinubu yana cikin barazanar kisa

Wanda ya fara bankado zargin alakar Dan Bello da Seyi Tinubu yana cikin barazanar kisa

  • Amnesty International ta ce ya zama dole a yi bincike game da abubuwan da Abdul Turaki ya fito yana kuka a kai
  • Matashin da yake gwagwarmaya ya fada wa duniya cewa ana yi masa barazana saboda maganganun da ya fada
  • Kafin yanzu ya fito ya zargi irinsu Dan Bello da yi wa Bola Tinubu aiki a boye alhali suna fafutukar Tinubu Must Go

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja – Kungiyar Amnesty International ta bukaci hukumomin tsaro su yi maza su binciki barazanar kisa da ake yi wa Mista Abdul Turaki.

An taso matashin ‘dan gwagwarmayan a gaba ne bayan ya fito yana zargin abokin tafiyarsu, Dan Bello da yi wa Mista Seyi Tinubu aiki a boye.

Daily Nigerian ta rahoto cewa Amnesty International ta yi kira ga hukuma da ta ba Andul Turaki kariya domin hadarin barazanar da ake yi masa.

A wani jawabi da ta fitar ranar Alhamis, kungiyar mai kare hakkin bil Adama a duniya ta nuna takaicinta game da barazanar da ake aiki ma shi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kai wa fitacciyar 'yar TikTok kuma 'yar Kwankwasiyya hari a Kano

Ana zargin cewa wasu sun fito suna zagin Abdul Turaki har ta kai ana yi masa barazanar amfani da karfin gwamnati domin a ga bayan matashin.

Hakan ta faru ne kusan mako guda kenan bayan ya yi zargin cewa gwamnatin kasar ta na kokarin sayen masu fafutukar Tinubu Must Go a Najeriya.

Da ya yi wani bidiyo ranar Laraba 25 ga watan Nuwamba 2026, Turaki ya shaida wa duniya rayuwarsa tana cikin hadari saboda tone-tonen da ya yi.

Amnesty ta fitar da jawabi tana cewa ya kamata wadanda alhakin kare jama’a yake wuyansu, su yi maza su binciki wannan zargi domin a kare shi.

“A wannan gaba, akwai nauyi da ya rataya a wuyan jami’an tsaro da su tashi da gaske kuma da wuri domin su yi gaggawar binciken ikirarin Abdul Turaki”

Sahara Reporters ta ce kungiyar ta kara da cewa dole a ba Turaki kariya, sannan kuma a dage sai an gano wadanda suke neman ganin bayan shi.

Amnesty ta ce bai dace a zura idanu alhali ana yi iwa mutane barazana irin haka ba, musamman idan ana kokarin rufe bakin masu sukar gwamnati.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

A jawabin, ita ma kungiyar ta duniya ba ta bayyana wadanda ake zargi da wannan mugun nufi ba.

Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga jami’an tsaro cewa an dauki mataki domin gano masu yi wa Turaki barazanar ko a ji cewa an ba shi kariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng