Uba Sani Ya Ƙara Kashewa Ƴan Arewa Guiwa saboda Tinubu a Zaɓen 2027
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bukaci shugabannin siyasar Arewa su hakura da neman shugabancin kasa a 2027, su fara shirin 2031
- Uba Sani ya ce Arewa na bukatar samar da cikakken tsarin ci gaba domin nuna shirinta na karbar mulkin Najeriya a 2031
- Gwamnan ya kalubalanci tsofaffin gwamnoni da mataimakan shugaban kasa da su bayyana ayyukan da suka yi wa jihohinsu da Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya shawarci shugabannin siyasar Arewa da su daina matsa lamba kan neman shugabancin Najeriya a zaben 2027.
Gwamna Uba Sani ya bukace su da su mayar da hankali wajen tsara dabarun da za su bai wa yankin damar karbar mulki a 2031.

Source: Twitter
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Kaduna, yayin wani taro da kungiyar Arewa Think Tank (ATT) da wasu kungiyoyin fararen hula suka shirya, cewar Punch.
Shawarar Uba Sani ga yan Arewa
Uba Sani ya ce ya kamata Arewa ta yi amfani da shekaru hudu masu zuwa wajen magance matsalolin ci gaba da suka addabi yankin, tare da tabbatar da cewa tana da shirin da zai ba ta damar jagorantar Najeriya..
Da yake magana kan shirin shugabannin Arewa na sake samar da shugaban kasa, gwamnan ya ce yankin na bukatar cikakken tsarin ci gaba maimakon dogaro da hujjar kasancewar dan takara dan Arewa.
Ya ce:
“Mu a Arewa, shin da gaske mun shirya? Mun tanadi komai? Da gaske muke yi? Wadannan tambayoyi ne da ya kamata mu yi wa kanmu domin samun amsoshi.”

Source: UGC
Bukatar da Uba Sani ya tura
Gwamnan ya kara da cewa ya bukaci masu neman shugabancin kasar da su fara aiki kan wani tsari tun yanzu, domin idan aka samu damar mika mulki ga Arewa a 2031, yankin ya kasance cikin shirin aiwatar da manufofinsa.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu
Sai dai ya bayyana cewa a halin yanzu Arewa ba ta shirya ba, saboda har yanzu babu wani cikakken tsarin da za ta dogara da shi wajen tafiyar da mulkin kasar, cewar Vanguard.
Haka kuma, Uba Sani ya soki yadda wasu 'yan siyasa ke neman goyon bayan jama'a bisa kasancewarsu 'yan wani yanki, yana mai cewa ya kamata a duba irin ayyukan da suka gudanar a lokacin da suke rike da mukaman gwamnati.
Ya ce:
“A lokacin da wasu suka fito suna magana kan zaben 2027, na rika tambayar kaina, wace kasa ce muke ciki? Wani ya ce a zabe shi saboda shi dan Arewa ne. Shin hakan yana da ma'ana? A'a!”
Gwamnan ya jaddada cewa lokacin yin alkawura kawai ya wuce, inda ya bukaci 'yan siyasa su fito da ayyukan da suka gudanar maimakon neman kuri'u da alkawuran da ba su tabbatar da su ba.
Uba Sani ya yi wa Tinubu alkawari
An ji cewa Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce APC za ta tattara ƙuri’u domin bai wa Shugaba Bola Tinubu kashi 70 cikin 100 a zaɓen 2027.
Ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APC ranar Alhamis.
Gwamnan ya ce gwamnatin Tinubu ta amince da manyan ayyukan raya ƙasa, ciki har da jami’o’i huɗu da tallafin N20bn ga Kaduna.
Asali: Legit.ng

