Kano Ta Dauki Zafi, Gwamnati Ta Maida Martani ga Kwankwaso kan Batun Binciken EFCC

Kano Ta Dauki Zafi, Gwamnati Ta Maida Martani ga Kwankwaso kan Batun Binciken EFCC

Kano, Nigeria - Gwamnatin Kano ta musanta zargin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya nemi Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta fara bincikensa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Gwamnatin ta bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba shi da wata alaƙa ko hannu a duk wasu harkokin da suka hada Kwankwaso da EFCC.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu ranar 27 ga Nuwamba, 2026 kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Gwamnatin ta ce tsohon gwamnan ya daɗe yana mu’amala da fuskantar bimcike daga hukumar yaƙi da cin hanci tun kafin gwamnatin yanzu ta hau mulki a Kano.

A cewa gwamnatin, bai dace Kwankwaso ya danganta Gwamna Abba da batun da ya faru tun kafin kafa gwamnatin yanzu ba.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262