Wani basarake ya kallubalance masu wa'azi kan yada zaman lafiya
- Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya yi kira ga masu wa'azin addinin musulunci su kasance masu yadda sakon zaman lafiya
- Sarkin ya yi wannan kiran ne a fadar sa yayin da mambobin kungiyar Markaz suka kai masa ziyarar ban girma
- Shugaban kungiyar, Dacta Yusuf Kolawole ya mika godiyar sa ga Sarkin bisa goyon baya da shawarwari da ya ke bawa yan kungiyar
Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya yi kira ga malaman addinin musulunci su rika amfani da wa'azin su wajen wanzar da zaman lafiya ke kyautata halayen al'umma kamar yadda yake cikin addinin muslunci.
Basaraken ya yi wannan kira ne a fadar sa yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar Markaz da suka kai masa ziyara karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Dacta Yusuf Kolawole a ranar Juma'a.
DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kwara ta yi wa malaman makaranta 13,931 karin girma
Sarkin ya jadada cewa ana iya samun cigaba da mai dorewa ne a kasar idan akwai zaman lafiya, hadin kai da kauna tsakanin al'ummar musulmi da sauran kabilu da addinai.
Ya kuma shawarci yan kungiyar suyi amfani da ilimin da suka samu wajen yada zaman lafiya a duk inda suka tsinci kansu. Ya kuma yaba da hangen nesa da kokari da wanda ya kafa kungiyar yayi, wato marigayi Sheikh Adam Abdullah Alilory musamman a yankin kudu maso yammancin Najeriya.
A jawabin da ya yi, sabon shugaban kungiyar, Dacta Yusuf Kolawole ya mika godiyarsa ga Sarkin na Ilori bisa goyon baya da shawarwari da ya ke bawa daliban makarantar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng