Labari mai dadi: Farashin shinkafa ya ragu da 25% a Maiduguri
- Farashin shinkafa da sauran kayayakin abinci ya sauka a kasuwannin garin Maiduguri
- A baya a kan sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogram 50 kan kudi N17,500 amma yanzu ana sayar da shi kan N15,000 - N16,500
- Yan kasuwar sun alakanta faduwar farashin kayayakin abincin da samun amfanin gona mai albarka da manoma sukayi a bana
Farashin shinkafar gida Najeriya a kasuwani ya ragu da 25%, hakan ya faru ne bayan girbe amfani gona da manoman shinkafa su ka yi cikin yan kwanakin nan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito.
Binciken da NAN ta gudanar a Gamboru da kuma kasuwan Unguwar Kwastam da ke Maiduguri ya nuna farashin ya sauka ne tun watanni biyu da suka wuce lokacin da manoma suka soma fida amfanin gona.
DUBA WANNAN: To fa! Anyi awon gaba da matashi, kuma aka yi ma sa auren dole
Buhun shinkafar na gida Najeriya ana sayar dashi kan N6,500 zuwa N7,200 a maimakon tsohon farashin N9,000 da a ke sayar wa a da. Faduwar farashin bai tsaya a shinkafar gida ba har ma shinkafar kasashen waje ta yi sauki.
A kwanakin baya a kan sayar da buhu mai nauyin kilogram 50 kan kudi N17,500 amma yanzu ana sayar da shi kan N15,000 - N16,500. Mudun shinkafar da ake sayar wa N1,050 a yanzu ana sayar da shi N900.
Farashin sauran kayan abinci ma duk sunyi sauki idan aka yi la'akari da yadda ake sayar da su watannin da suka shude. Yan kasuwa sun alakanta faduwar farashin ga yadda aka samu karin kayayaki a kasuwannin saboda manoma sun girbe amfanin gona kuma suna shigo da su kasuwani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng