Ana rigima a cikin gidan Sanata Danjuma Goje
- Tsohon surukin Sanata Danjuma Goje ya kai Sanatan da diyar shi kara kotu inda yake bukatar su dawo masa da yar sa
- Tsohon Surukin Sanatan, Abubakar Faruk ya bukaci kotun ta tilastawa Sanata Goje da uwar yar su dawo daga ita daga birnin Landan domin ta dawo Najeriya ta cigaba da karatu
- Faruk kuma ya bukaci kotun ta haramtawa Surukun nasa fita da yaran wajen garin Abuja ba tare da neman izinin sa ba
Babban manajan kamfanin kula da kasuwar Babban Birnin Tarayya Abuja, (AMML) kuma tsohon surukin Sanata Danjuma Goje, Abubakar Faruk ya shigar da kara a kotu inda ya ke bukatar kotun ta tabbatar masa da cikakiyar ikon renon yar ta suka haifa lokacin yana auren diyar Gojen.
A cikin karar da ya shigar a kotun Area 1 da ke Abuja, Faruk ya na neman kotu ta tursasa tsohon surukin nasa, Sanata Goje da tsohuwar matar nasa Fatima su dawo da yar ta sa daga birnin Landan domin ta dawo gida Najeriya ta cigaba da karatu a jami'ar Nile da ke Abuja.
DUBA WANNAN: Sojoji sun yiwa shugaban kungiyar Boko Haram babban lahani
Faruk dai auri Fatima ne a ranar 20 ga watan Disambar 1997, kuma bayan auren sun haifi yara uku. Maza biyu da mace daya kafin ya mutu a ranar 31 ga watan Augustan 2014. Faruk ya shaida wa kotu cewa tsohuwar matar ta sa da surukin sa ne suka hada baki wajen tafiya da diyar Birnin Landan.
Faruk yana fata kotun za ta hanna surukan nasa fita da yaran daga garin Abuja ba tare da neman izinin sa ba sai dai lauya mai kare surukan nasa, Kennedy Anoba ya kallubalanci bukatar na Faruk inda ya ce kotun ba ta da damar cewa komai kan lamarin tunda yar tana kasar waje.
Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Janairu 2017.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng