Dattawan Arewa Sun Fadawa Tinubu Dalilin da Suka Jawo ake Fushi da Shi
- Kungiyar ACF ta ce tabarbarewar rayuwa, karuwar talauci da matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da ke jawo fushin jama'a kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Mai magana da yawun kungiyar, Tukur Mohammed-Baba, ya ce rashin jin dadin jama'a ba ya shafar Arewa kadai, domin matsalolin sun bazu a sassan Najeriya
- A wata sanarwar da ya fitar, Mohammed-Baba ya kuma yi gargadin cewa bai kamata a danganta fushin jama'a da bambancin addini ko yankin da suka fito ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mai magana da yawun kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Tukur Mohammed-Baba, ya bayyana cewa tsadar rayuwa, talauci da rashin tsaro na daga cikin manyan dalilan da ke jawo fushin 'yan Najeriya kan gwamnatin Bola Tinubu.
Ya ce rashin jin dadin jama'a ba ya shafar Arewa kadai, yana mai cewa matsalolin da ake fuskanta a kasar sun shafi 'yan Najeriya daga dukkan yankuna.

Source: Facebook
Tukur Mohammed-Baba ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV kan lamuran yau da kullum.
Maganar ACF kan tsadar rayuwa
Mohammed-Baba ya yi gargadin cewa danganta fushin jama'a da bambancin Arewa da Kudu ko addini na iya karkatar da hankali daga ainihin matsalolin da kasar ke fuskanta.
Ya ce abin da ya fi dacewa shi ne a fahimci cewa 'yan Najeriya ne ke nuna rashin jin dadinsu, ba wai mutanen wani yanki kadai ba.
Ya kara da cewa ana iya ganin wannan fushi a lokacin gangamin siyasa a sassa daban-daban na kasar, inda aka samu zanga-zanga, arangama da wasu alamomin nuna rashin amincewa.
Sai dai ya amince cewa Arewa na nuna fushin siyasa sosai, wanda ya danganta da tabarbarewar tattalin arziki da matsalar tsaro.
Rashin tsaro ya kawo cikas
Mai magana da yawun ACF ya ce yanayin rayuwa ya kara tsananta, talauci ya karu, sannan mutane da dama na fuskantar wahalar samun abin da za su ci.
Daily Trust ta wallafa cewa ya bayyana cewa rashin tsaro ya kawo cikas ga noma da sauran harkokin tattalin arziki, musamman a yankunan da manoma ke fama da hare-hare da sauran matsalolin tsaro.
Ya kuma ce durkushewar wasu masana'antun sarrafa amfanin gona ta kara rage damar samun ayyukan yi da hanyoyin samun kudin shiga a yankin.

Source: Getty Images
A yayin hirar, Mohammed-Baba ya ba da misalin wata mata daga jihar Adamawa da ta koka kan yadda ake sayar da buhun masara da shinkafa a kan Naira 30,000 zuwa Naira 35,000, yayin da buhun taki ya haura Naira 60,000.
Maganar kayar da Tinubu a 2027
A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar da ya fi saukin kayarwa a zaben 2027.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Baba-Ahmed ya ce idan aka gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci, Tinubu zai sha kaye a jihohi da dama a Najeriya.
Ya kuma zargi wasu mutanen da ke kewaye da shugaban kasar da yi masa bayanan karya kan damar da yake da ita ta sake lashe zabe.
Asali: Legit.ng

