Hadimin Tinubu Ya Hada Kwankwaso da Obi Ya Yi Masu Rubdugu kan 2027

Hadimin Tinubu Ya Hada Kwankwaso da Obi Ya Yi Masu Rubdugu kan 2027

  • Daniel Bwala ya yi watsi da yiwuwar Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasa na 2027, yana mai cewa tsohon gwamnan Anambra ya fi samun karbuwa a kafafen sada zumunta
  • Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa ta siyasa ya ce farin jinin Obi a intanet ba yana nufin zai samu nasara a akwatin zabe ba
  • Bwala ya kuma yi ikirarin cewa yanayin siyasar da ya taimaka wa Obi a zaben 2023 ya sauya kuma Rabiu Kwankwaso ma ya san ba za su yi nasara a zaben 2027 da ke tafe ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ba shi da damar lashe zaben shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala zai fara yakin neman zabe, yana tunanin ya tafi da Atiku Abubakar a ADC

Ya bayyana Obi a matsayin shugaban kafafen sada zumunta, yana mai cewa ba wanda zai iya yin gogayya da shi wajen samun farin jini a intanet.

Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a taron NDC. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV ranar Alhamis.

Bwala ya caccaki Peter Obi

Da aka tambayi Bwala wadanda yake ganin ba su da damar lashe zaben 2027, ya ambaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da wasu da ya kira masu kirkirar abubuwan da ake yadawa a kafafen sada zumunta.

Da aka nemi ya bayyana wadanda yake nufi, sai ya ambaci Peter Obi, yana mai cewa shi da magoya bayansa sun mayar da hankali wajen kirkirar abubuwan da za su jawo hankalin jama'a a intanet.

Ya ce:

“Mun dade da sanin cewa shi ne shugaban kafafen sada zumunta. Babu wanda yake gogayya da shi a wannan fanni.”

Bwala ya ce syasa ta sauya a 2027

Da aka tambaye shi game da kuri'u miliyan 6.1 da Obi ya samu a zaben shugaban kasa na 2023, Bwala ya ce tsohon gwamnan ya amfana da goyon bayan Kiristoci a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

A cewarsa, goyon bayan da Obi ya samu ya samo asali ne daga yadda wasu Kiristoci suka mayar da martani ta hanyar zaben wanda suke ganin zai wakilce su.

Bwala ya kuma yi ikirarin cewa yawancin mu'amalar Obi a cikin shekaru hudu da suka gabata sun fi karkata ga zuwa majami'u.

Daniel Bwala
Hadimin Tinubu, Daniel Bwala. Hoto: Daniel Bwala
Source: Facebook

Bwala ya caccaki Kwankwaso

Bwala ya kuma yi ikirarin cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya hada kai da Obi ne saboda burinsa na takarar shugaban kasa a 2031.

A cewarsa, Kwankwaso ya san cewa Obi ba zai lashe zaben 2027 ba, amma yana ganin hadin gwiwar zai taimaka masa wajen samun goyon bayan al'umma daga sassa daban-daban.

Ga bayanin da Bwala ya yi a kan Kwankwaso:

An farmaki tawagar Obi

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun bude wa jama'a wuta yayin wani gangamin yakin neman zaben Peter Obi na jam'iyyar NDC a jihar Edo.

Rundunar 'yan sandan jihar Edo ta ce ta fara farautar wadanda suka kai harin, tare da kara jami'an tsaro a yankin da lamarin ya faru domin tabbatar da tsaro.

Harin ya zo ne kwanaki kadan bayan kashe wasu mutane a wani taron jam'iyyar NDC a jihar Delta, inda jami'an tsaro suka yi alkawarin gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng