An kamalla hada sakamakon jarabawar mutane 43,000 masu neman aikin malanta a jihar Kaduna - El-Rufa'i
- Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, shi ne ya bayar da wannan sanarwar
- Ya kuma tabbatarwa duk wani malamin Jihar da ya yi yajin aiki fuskantar hukunci
- Ya kuma ce su na nan kan bakan su wurin dawo da martabar ilimi a Jihar
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya sanar da cewan sun kammala hada sakamakon jarabawar mutane 43,000 da su ka nemi aikin koyarwa a makarantun firamari na Jihar. Ya yi wannan bayani ne ranar Litini ta bakin mai magana da yawun sa, Samuel Aruwan.
Ya kuma yabawa malamai da su ka cigaba da zuwa wuraren ayyukan su duk da haramtacciyar yajin aikin da Kungiyar Malamai ta NUT ta kudiri aniyar yi.
KU KARANTA: Sojin Najeriya ta mika 'yar Chibok ga gwamnatin jihar Borno
Gwamnan ya kuma tabbatarwa duk wani malami da ya kauracewa aikin sa ko ya kawo cikas ga aikin wanin sa, fuskantar hukunci kamar yadda doka ta tanadar.
A cewar sa, ba za su bari son rai na tsirarun mutane ya cutar da 'ya'yan talaka guda miliyan 2 ba. Don haka su na nan kan bakan su na tabbatar da sun kawo gyara kuma sun kawar da gurbatattun malamai.
Yanzun da a ka kammala hada sakamakon jarabawar masu neman aikin koyarwar, za a wuce zuwa mataki na gaba na daukan malaman guda 25,000, in ji shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng