Sojin Najeriya ta mika 'yar Chibok ga gwamnatin jihar Borno

Sojin Najeriya ta mika 'yar Chibok ga gwamnatin jihar Borno

- Rundunar Soji ta Operation Lafiya Dole ce ta tseratar da ita a ranar 4 ga watan Janairu

- Rundunar ta mika ta zuwa ga hannun Mataimakin Gwamnan Jihar a Maiduguri

- Ya zuwa yanzun, an tseratar da 'yammatan Chibok fiye da 100

A ranar Talata ne Hukumar Sojin Najeriya ta danka yarinyar Chibok mai suna Solomi Pogu, zuwa ga Gwamnatin Jihar Borno. Pogu ta na daga cikin 'yammata 219 da 'yan Boko Haram su ka sace su daga makarantar su a 2014.

Kwamandan Rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas, shi ne ya mika ta hannun Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Usman Durkwa, a Maiduguri .

Hukumar Soji ta mika yarinyar Chibok da aka ceto ga gwamnatin Borno
Hukumar Soji ta mika yarinyar Chibok da aka ceto ga gwamnatin Borno

DUBA WANNAN: Wani dan Majalisar Tarayya ya fice daga APC

Nicholas ya ce rundunar ta su da ke aiki a Pulka na karamar Hukumar Gwoza, ita ce ta tseratar da ita tare da wata mai suna Jamila Adams, a ranar 4 ga watan Janairu. Ya yi kira da a yi wa 'yammatan rejistar da ta dace kafin a mika su hannun iyayen su.

Durkwa a yayin karban 'yammatan, ya yabawa Soji na jajircewar su don ganin sun kwato 'yammatan na Chibok. Ya kuma yi fatan za a tseratar da ragowar 'yammatan nan ba da jimawa ba daga hannun Boko Haram.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ta ruwaito cewan 'yammata 219 ne a ka sace a Makarantar Sakandare ta 'Yammata na Chibok a 2014. A halin yanzun dai an tseratar da fiye da 100 daga cikin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: