Rikicin Shugabanci: Kotu Ta ba da Umarnin Kama Babban Malami a Najeriya

Rikicin Shugabanci: Kotu Ta ba da Umarnin Kama Babban Malami a Najeriya

  • Kotu ta ba da umarnin a kamk mata Fasto Jimmy Odukoya saboda gaza bayyana a gabanta duk da sammacin da ata aika masa
  • Mai shari’a O. Adewunmi-Oshin ce ta bayar da umarnin a ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026, bayan Odukoya bai halarci zaman kotun ba
  • Wannan mataki ya biyo bayan rashin halartar zaman kotu da malamin ya yi kan shari'arda ta shafi rikicin cocinsu ta Fountain of Life.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Babbar Kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikoyi ta bayar da sammacin kama Fasto Jimmy Odukoya saboda gaza bayyana a gabanta a shari’ar da ta shafi rikicin shugabanci a cocin The Fountain of Life.

Mai shari’a O. Adewunmi-Oshin ce ta bayar da umarnin a ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026, bayan Odukoya bai halarci zaman kotun ba a shari’ar da amintattun cocin suka shigar.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya tube babbar riga ya tafi kotu kare El Rufa'i

Jimmy Odukoya
Babban malami a cocin Fountain of Life, Fasto Jimmy Odukoya Hoto: Jimmy Odukoya
Source: Instagram

Alƙalin ta kuma bayar da umarnin mayar da takardun shari’ar ga alƙalin gudanarwa domin sake tura ta ga wani alƙali, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Wannan sammacin kama Fasto Odukoya ya biyo bayan wani umarnin kotu da Mai shari’a Adewunmi-Oshin ta bayar a ranar 18 ga Nuwamba, inda ta hana shi gabatar da kansa a matsayin babban malamin coci kuma shugaban cocin Fountain of Life.

Yadda rikicin shugabanci ya fara

Rikicin shugabancin cocin ya fito fili ne a ranar 17 ga Nuwamba, lokacin da wani ɓangare na kwamitin amintattun cocin ya sanar da cire Odukoya daga mukaminsa.

Sun ce sun yi la’akari da sake duba kundin tsarin mulkin cocin da kuma wani faifan bidiyo da aka ɗauka a watan Disamba na 2021.

A cikin bidiyon, marigayi wanda ya kafa cocin, Fasto Taiwo Odukoya, ya bayyana Fasto Kunle Areogun a matsayin wanda yake so ya gaje shi, yayin da ya ware wa Jimmy ayyukan kula da matasa da gudanarwa.

Kara karanta wannan

An kama mai shiga makabarta yana cire likkafani a jikin gawar da aka birne

Bayan sanar da cire shi, amintattun sun naɗa Fasto Rotimi Okpaise a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na harkokin ibada da gudanarwar cocin.

Sai dai Odukoya ya ƙi amincewa da cire shi, yana mai cewa an amince da naɗin da aka yi masa a watan Satumba na 2023 bayan rasuwar mahaifinsa, kuma har yanzu shi ne halastaccen babban limamin cocin.

Fasto Odukoya ya garzaya kotu

A martanin da ya mayar kan matakin kwamitin, Odukoya ya shigar da wata kara dabam a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.

Ya shigar da ƙarar ne a kan ’yar’uwarsa, Fasto Tolu Odukoya-Ijogun, da wasu mambobin cocin guda bakwai, inda yake neman kotu ta soke ƙudurin da ya cire shi daga mukaminsa.

Fasto ya gano dalili rura wutar matsalar tsaro

Kun ji cewa Shugaban Majalisar Manyan Bishof-bishof ta Najeriya, Archbishop Leonard Bature Kawas, ya zargi wasu masu hannu a daukar nauyin ta'addanci.

Fitaccen limamin cocin ya zargi wasu mutane da daukar nauyin ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci domin bata sunan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262