Dan sanda ya rasu, wasu sun jikata sakamokon hatsarin da ta rutsa da tawagar Gwamna Ishaku
- Dan sandan mai kula da matar Gwamnan ya yi hatsarin ne cikin motar sa kirar SUV
- Cikin motar dauke ya ke da abokan aikin sa mata guda biyu
- Hatsarin ya faru ne a kan hanyar Bali ta jalingo yayin da tayar motar ta fashe
Labari ya zo mana daga jaridar Punch cewar dan sandan farin kaya (CIB), da ke yi wa matar Gwamnan Jihar Taraba, Anna Darius Ishaku hidima, ya rasa ransa yayin da motar sa wacce ke cikin tawagar Gwamnan, ta yi hatsari.
Hatsarin ya faru ne da misalin 4:45 na yamma, a kan hanyar Bali na Jalingo, yayin da Gwamnan ke dawowa daga Takum, inda a nan ne ya yi hutun kirismeti da ta sabuwar shekara.
KU KARANTA: Kungiyar musulunci ta bukaci a canja dokar hana saka hijabi a makarantun horas da lauyoyi
Wata 'Yar Sandan ta CIB da wata Malamar Asibiti da su ke cikin motar sun jikkata sosai, a inda su ke cikin matsanancin hali yayin tattara wannan bayani. Su biyun duk jami'ai ne ma su yi wa matar Gwamnan hidima.
Wata majiya ta shaida cewar motar wacce kirar SUV ce, ta na daga can baya, tawagar Gwamnan ta yi mata nisa. Majiyar ta ce hatsarin ya faru ne sakamakon tayar motar ta fashe.
ASP David Mishal na Hukumar 'Yan Sanda da ya yi magana da yawun Hukumar, ya tabbatar da faruwar hatsarin. Sai dai ya ce ba shi da masaniyar an rasa rai. Ya ce sa zaran ya tabbatar da hakan zai sanar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng