Gobara ta lashe gonan rake mai fadin hecta 30 a jihar Kebbi
- Gobarar ta afku ne a daren Alhamis bayan manoman sun tafi gidajen su
- Shugaban karamar hukumar ya ce manoman sunyi asarar dukiyar da ta tasar ma miliyoyin naira sakamakon gobarar
- Shugaban hukumar agajin gagawa na jihar (SEMA), Alh. Rabiu Kamba ya ziyarci gonar kuma ya ce gwamnati zata tallafawa manoman da abin ya shafa
Gobara ta cinye wata gonan rake mai fadin hecta 30 a kauyen Mai-Ramu da ke karamar hukumar Koko/Besse da ke jihar Kebbi. Shugaban karamar hukumar, Alhaji Shu'aibu Ibrahim ne ya bayyana wa kamfanin dillanci labarai (NAN) a ranar Juma'a cewa anyi asarar tsirai na miliyoyin naira.

DUBA WANNAN: Wani basarake ya kallubalance masu wa'azi kan yada zaman lafiya
Shugaban karamar hukumar ya cigaba da cewa gobarar ta faru ne a daren Alhamis bayan manoman sun tafi gidajen su, hakan ya sa babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar, Kauyen na Mai-Ramu yana daya daga cikin garuruwan da ke kan gaba wajen noman rake.
A yayin da ya ziyarci inda gobarar ta faru, shugaban hukumar agajin gagawa na jihar (SEMA), Alhaji Rabiu Kamba ya jajinta wa manoman bisa asarar da sukayi.
Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta tallafa wa manoman domin su rage radaddin asarar da ta same su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng