Ku zama masu adalci ga Islama da Musulmi: Kungiyar 'yan jarida musulmi ta fadawa kafafen watsa labarai
- Kungiyar musulmi ma'aikatan kafafen yada labarai na kasa (MMPN) ta yi ikirarin cewa ana cin zarafin musulunci da musulmai a kafafen yadda labarai
- Kungiyar ta ce hakan na faruwa ne domin galibin masu aiki a kafafen yadda labaran ba musulmi bane
- Masani addinin musulunci kuma mai rajin kare hakin bil adama, Lakin Akintola ya yi kira ga Kungiyar yan Jarida na kasa (NUJ) ta kafa dokokin da zasu hukunta yan jaridar da ke yadda kareraki
Musulmin ma'aikatan kafafen yadda labarai sunyi kira ga kafafen yadda labaran Najeriya su dena yadda rahotonin batanci kan musulmi da musulunci a kafafen yadda labarai. Hakan yana daga cikin yarjejeniyar da aka cinma tsakanin malaman addinin da yan jaridar a taron 'Muslim Media Practioners of Nigeria' (MMPN) reshen jihar Legas.
A yayin da yake jawabi a wajen taron, Lied Tella, gogagen dan jarida ya lura cewa ba'a yiwa musulunci da musulmai adalci wajen rahotanni a kafafen yadda labarai domin mafi yawancin ma'aikatan yadda labaran ba musulmi bane.
DUBA WANNAN: Da duminsa: Wata kotun tarayya ta soke hukuncin dakatarwar da jam'iyyar PDP ta yiwa wani Sanata
A kasidar da ya gabatar wajen taron, Tella ya kallubalanci yan jarida musulmi su dage wajen farfado da martaba da mutuncin addinin musulunci ta hanyar nuna kwarewa wajen aiki. Tell dai babban manazarci ne a sashin koyar aikin jarida a jami'ar Ilori.
Farfesa Lakin Akintola, masannin addinin musulunci kuma mai rajin kare hakin bil-adama ya zargi kafafen yadda labaran Najeriya da rashin yiwa musulmi da musulunci adalci wajen cikin rahotanni da labarai da suke yadawa.
Farfesa Akintola yayi kira ga musulimin Najeriya su dage wajen bude kafafen yadda labarai, ya kuma shawarci Kungiyar yan jarida na kasa (NUJ) ta kafa dokoki na hukunta duk dan jaridar da ya yadda labaran karya da gangan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng