Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
A ziyarar aiki da ya kawo na kwanaki biyu a Jihar Jigawa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin tafkin Hadejia domin amfanin manoman rani, wanda aka ƙaddamar a Ƙaramar Hukumar Auyo da wasu ayyukan.
Babayaro wanda ya kasance daya daga cikin 'yan wasan da suka buga wasa tsakanin Niger Tonardoes da Kwara United a ranar Lahadi 13 ga watan Mayu, ya rasu ne a jiya Litinin 14 ga watan Mayu bayan yayi hatsari a daidai kofar gidansu.
A ranar Litinin, 14 ga watan Mayu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata rarrabawa yan Najeriya dala miliyan 320 wanda Abacha ya sata ya boye a kasashen ketare a lokacin da yake shugabancin kasa.
Kotu ta 7 a garin Umuahia ta tura wasu mutane tara gidan yari wadanda aka kama a gidan shugaban kungiyar inyamurai ta Biafra, Nnamdi Kanu, sun kuma fuskanci zargin ta’addanci, satar mutane da kuma garkuwa da mutane.
Gwamnatin Kasar Falasdin ta sanar da cewa, amfani da uzurin taruka wajen hana kiran Sallah a Birnin Kudus take hakkin Addini ne ga Musulmai. Ministan Al'amuran Addini Kungiyoyi Yusuf Edis ya bayyana cewa, su ba suyi na’am da hakan
Jami’an ‘yan sanda a karamar hukumar Suleja, dake Jihar Nige sun damke iyayen wata amarya sakamakon kin tarewa a gidan mijin, da aka daura musu aure. Ango mai suna Shuaibu Dauda ne ya kai karar, ya ce sa’o’i kadan bayan daura aure
A ranar Litinin, 14 ga watan Mayu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziyya ga shugaban cocin Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare akan mutuwar mahaifiyar Faston marigayiya Misis Abigail Eebudola Bakare.
Kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus-Sunna (JIBWIS) a jiya ta rarrabawa malamai kusan 201 kayayyakin kusan N3m na shinkafa da Sikari gabanin shigowar watan Ramadan. Anyi hakan ne don kara karfafa masu gwiwa.
A sanarwar da sashen tarban baki na gidan gwamnati ta bayar tace ana sanya ran shugaban kasar zai sauka a filin jirgin saman Dutse da misalin karfe goma na safe inda zai wuce zuwa garin Auyo domin kaddamar da aikin noman rani.
Aisha Musa
Samu kari