‘Mun Gama da Su’: Trump a Fadi Yadda Ya Kawo Karshen Kisan Kiristoci a Najeriya

‘Mun Gama da Su’: Trump a Fadi Yadda Ya Kawo Karshen Kisan Kiristoci a Najeriya

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana game da hare-haren sojin Amurka da ya kawo a Najeriya wanda ya ce ya yi tasiri
  • Trump ya bayyana cewa hare-haren sun kashe shugabannin kungiyar ISIS/ISWAP da dama, tare da rage karfin kungiyar wajen kai hare-hare
  • Ya kuma ce gwamnatin sa za ta ci gaba da farautar ‘yan ta’adda a ko’ina, tana mai jaddada kudirin kare ‘yancin addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana jin dadinsa game da kai hare-haren makamai masu linzami a Najeriya.

Shugaba Trump ya ce hare-haren sun ceci al’ummar Kiristoci daga hare-haren masu akidar ta’addanci.

Trump ya fadi yadda ya kare Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Amurka, Donald Trump. Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a birnin Washington wanda shafin Fox News ya bibiya.

Kara karanta wannan

Trump ya tsokano sabon fada, Iran ta kai hare haren kan Amurka

Trump ya magantu kan hari a Najeriya

Trump ya ce kafin hare-haren, dubban mutane da suka hada da yara, mata da tsofaffi suna rasa rayukansu a hannun ‘yan ta’adda.

Ya ce matakin da Amurka ta dauka ya taimaka wajen rage yawan hare-haren da ake kai wa fararen hula.

A cewarsa, hare-haren sun yi wa kungiyoyin ta’adda mummunar illa, inda aka kashe shugabansu na farko, na biyu da kuma na uku.

Ya ce hakan ya sanya sauran mayakan tsoro tare da rage shirinsu na kai farmaki.

Trump ya kwatanta aikin da aka gudanar a Najeriya da wasu matakan soja da Amurka ta dauka kan Iran.

Trump ya bayyana yadda harinsa a Najeriya ya nakasa yan ta'adda
Shugaban kasar Amurka Donald J Trump Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Trump ya magantu kan nukiliyar Iran

Trump ya ce gwamnatinsa ba za ta bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, ya kara da cewa yana kokarin kare Kiristoci a sassa daban-daban na duniya.

Shugaban Amurkan ya ce kasarsa za ta ci gaba da bibiyar ‘yan ta’adda a duk inda suke.

Kara karanta wannan

'Isra'ila ta hallaka dubban yara kanana da gangan a Falasdinu'

Ya ce Amurka na amfani da manyan makamai wajen kai hare-hare domin kawar da barazanar tsaro.

Trump ya yi gargadin cewa akwai bukatar kare ‘yancin addini, yana mai cewa dole ne a dakile duk wani yunkuri da zai iya hana mutane gudanar da addininsu cikin ‘yanci.

Daga baya kuma an gudanar da wasu hare-hare hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka a Borno, cewar Vanguard.

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa hare-haren hadin gwiwar sun kashe mayakan ISIS/ISWAP da dama a yankunan Metele da Arege da ke Borno, tare da raunana ayyukansu.

Trump ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da abokan hulda wajen yakar ta’addanci, domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya da kare rayukan fararen hula.

Tinubu ya magantu kan barazanar Trump a Najeriya

A baya, mun ba ku labarin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su kwantar da hankulansu kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

Ministan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce shugaban ƙasa na tattaunawa da ƙasashen duniya don kare martabar Najeriya.

Gwamnati ta ce fara daukar wadansu matakai don inganta tsaro a ƙasa bayan kalaman Donald Trump na cewa ana kisan kiristoci zalla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.