Ramadan: Buhari ya aika sakon gaisuwa ga Musulmai, ya bukaci da su nuna soyayya ga yan Adam
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalubalancin al’umman Musulmi da suyi amfani da damar da Ramada ya kawo wajen kara soyayyarsu ga yan Adam, ayyukan sadaka, kyautatawa, aminci da kuma godiya.
Shugaban kasar ya kalubalance su ne a sakon Ramadan day a aika ga Musulmai ta baki kakakinsa Malam Garba Shehu a Abuja a ranar Laraba, 16 ga watan Mayu.
Shugaba Buhari wanda ya yi gaisuwa ga Musulman Najeriya daman a duniya baki daya yayinda suka fara azumin Ramadana wanda ke shafe tsawon kwanaki 30 ya bayyana cewa watan Ramadan ya kasance lokaci da maida hankali ga ibadah da kuma nutsuwa.
A cewarsa azumi ba wai yana nufin mutun ya kasance cikin yunwa da kishirwa kawai bane, sai dai ya kasance dama da mutun zai tsarkake zuciyarsa da kuma ayyukansa.
Ya bayyana cewa annabi Muhammad ya kasance yana alkhairi sosai ga talakawa da mabukata a irin wannan lokaci.
Don haka shugaban kasar ya bukaci Musulmai a kasar dama fadin duniya da suyi koyi da kyawawan dabi’u.
KU KARANTA KUMA: Ramadan: Sunaye da fuskokin wasu fitattun 'yan kwallon Duniya 30 da za su yi azumi
Yayi kira ga dukannin yan Najeriya das u tuna maza da mata da basu kaisu karfi ba a koda yaushe sannan kuma su taimakawa gwamnati wajen magance kalubalen da take fuskanta a kasar.
Yayi addu’a ga Allah ya ba Musulmai karfin kammala azumin wannan wata.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng