Yanzu Yanzu: Ganduje ya magance rikicin dake faruwa a majalisar jihar Kano

Yanzu Yanzu: Ganduje ya magance rikicin dake faruwa a majalisar jihar Kano

- Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya daidaita tsakanin ‘yan majalisar jihar daketa hatsaniya a tsakaninsu

- Kwamishinan labarai, Mohammed Garbage yace an gudanar da taron daidaitawar ne a jiya a gidan gwamnatin jihar Kano a tsakanin ‘yan majalisun da kuma gwamna Abdullahi Umar Ganduje

- Garba, yace gwamna Ganduje ya shiga tsakanin ‘yan majalisar ne domin ya kawo zaman lafiyaa majalisa da kuma cigaban siyasar jihar

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya daidaita tsakanin ‘yan majalisar jihar daketa hatsaniya a tsakaninsu.

Kwamishinan labarai, Mohammed Garba yace an gudanar da taron daidaitawar ne a jiya a gidan gwamnatin jihar Kano a tsakanin ‘yan majalisun da kuma gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Yanzu Yanzu: Ganduje ya maganace rikicin dake faruwa a majalisar jihar Kano
Yanzu Yanzu: Ganduje ya maganace rikicin dake faruwa a majalisar jihar Kano

Garba, yace gwamna Ganduje ya shiga tsakanin ‘yan majalisar ne domin ya kawo zaman lafiyaa majalisa da kuma cigaban siyasar jihar, “majalisar zata dawo zama a ranar Alhamis, don kara tattaunawa da samun mafita game da matsalar da suke fuskanta a tsakaninsu.”

KU KARANTA KUMA: An gano shugaba Buhari a kasuwa tare da gwamnan jihar Jigawa (hoto)

Majiya ta bayyana cewa Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya kawo karshen rikicin tsakanin kungiyar majalisar da suka rabu biyu suna rikici a tsakaninsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng