Gwamnatin Jigawa ta karya farashin buhun shinkafa ga ma’aikata domin yin azumi cikin walwala

Gwamnatin Jigawa ta karya farashin buhun shinkafa ga ma’aikata domin yin azumi cikin walwala

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin jihar Jikawa karkashin shugabancin Gwamna Badaru ta siyo buhuhunan shinkafa mai dumbin yawa domin ta rarrabawa ma’aikatan jihar bashi kan farashi mai rahusa inda za su biya cikin watanni biyu.

Bisa ka’ida ana siyar da buhun shinkaa akan naira 14,000 a kasuwa inda ita kuma gwamnatin Jigawar ta baiwa ma’aikata bashi akan naira 12,000 sannan kuma zasu biya kudin ne cikin watanni biyu.

Haka zalika an bayyana cewa ana rarraba wannan shinkafa ne a dukannin kananan hukumomi dake fadin jihar.

Gwamnatin Jigawa ta karya farashin buhun shinkafa ga ma’aikata domin yin azumi cikin walwala
Gwamnatin Jigawa ta karya farashin buhun shinkafa ga ma’aikata domin yin azumi cikin walwala

Gwamna Badaru ya fiddo da wannan shiri ne domin tallafawa al'ummar jihar duba da watan azumi da aka shiga domin kowa yayi azumi a cikin farin ciki da annashiwa.

KU KARANTA KUMA: Shugaban hukumar ‘Yan Sanda na kasa ya zargi Saraki da son janye hankali daga lamarin ‘yan ta’addan da aka dauka haya

Har ila yau kuma Gwamnan ya dauki aniyar baiwa dukkanin ma'aikatan Jihar Jigawa kudin hutun su a cikin wannan watan domin ganin kowa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin wannan wata mai tarin albarka na Ramadana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel