An kama mabiya addinin Yahudawa a gidan Kanu, an kuma gurfanar dasu a gaban kotu bisa laifin ta’addanci

An kama mabiya addinin Yahudawa a gidan Kanu, an kuma gurfanar dasu a gaban kotu bisa laifin ta’addanci

- Kotu ta 7 a garin Umuahia ta tura wasu mutane tara gidan yari wadanda aka kama a gidan shugaban kungiyar inyamurai ta Biafra, Nnamdi Kanu, sun kuma fuskanci zargin ta’addanci, satar mutane da kuma garkuwa da mutane

- Masu gabatar da kara sun bayyana cewa wanda ake zargin sunyi yunkurin tsoratar da ASP Justus Ogar da mutanensa, wanda laifi ne da ya sabawa sashe na 12(a) na dokar jihar Abia

- Mai kare wadanda ake zargin Joshua iheohunkara Chinoye, ya roki kotun da ta bayar da wadanda yake karewa akan beli sakamakon laifin da ake zarginsu da aikatawa ba wanda ya sabawa dokar kasa bane

Kotu ta 7 a garin Umuahia ta tura wasu mutane tara gidan yari wadanda aka kama a gidan shugaban kungiyar inyamurai ta Biafra, Nnamdi Kanu, sun kuma fuskanci zargin ta’addanci, satar mutane da kuma garkuwa da mutane.

Masu gabatar da kara sun bayyana cewa wanda ake zargin sunyi yunkurin tsoratar da ASP Justus Ogar da mutanensa, wanda laifi ne da ya sabawa sashe na 12(a) na dokar jihar Abia, ta ta’addanci, satar mutane da kuma garkuwa da mutane, sai kuma amfani da makamai don tsoratarwa.

An kama mabiya addinin Yahudawa a gidan Kanu, an kuma gurfanar dasu a gaban kotu bisa laifin ta’addanci
An kama mabiya addinin Yahudawa a gidan Kanu, an kuma gurfanar dasu a gaban kotu bisa laifin ta’addanci

Mai kare wadanda ake zargin Joshua iheohunkara Chinoye, ya roki kotun da ta bayar da wadanda yake karewa akan beli sakamakon laifin da ake zarginsu da aikatawa ba wanda ya sabawa dokar kasa bane.

KU KARANTA KUMA: Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari

Yace wadan da ake zargin an kamasu ne a wurin bautar tare da matayensu da yaransu wadanda kuma duk suna cikin kotun a lokacin da ake sauraren shari’ar, inda sukayi ikirarin cewa duk wadannan laifuka da ake zarginsu da aikatawa babu yanda za’ayi su aikatasu a gaban matayensu da yaransu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng