Dan kwallon Niger Tonardoes, Isa Hussaini ya rasu bayan watanni 2 da aurensa
Allah yayiwa hazikin dan kwallon kafa na kingiyar Niger Tonardoes, Isa Hussaini wanda aka fo sani da Babayaro rasuwa.
Babayaro wanda ya kasance daya daga cikin 'yan wasan da suka buga wasa tsakanin Niger Tonardoes da Kwara United a ranar Lahadi 13 ga watan Mayu, ya rasu ne a jiya Litinin 14 ga watan Mayu bayan yayi hatsari a daidai kofar gidansu dake yankin Rukunin Gidaje na Flamingo dake yankin Maitunbi a garin Minna, babban birnin jihar Niger.
Rahotanni sun nuna cewa wani mai babur ne ya buge shi inda bayan an yi gaggawar kai shi asibiti ya rasu.
KU KARANTA KUMA: Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari
Marigayin ya rasu ya bar iyayensa da 'yan uwa da matarsa wadda ba su wuce wata biyu da yin aure ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng