Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari

Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya ce gwamnatin tarayya zata rarrabawa yan Najeriya dala miliyan 320 wanda Abacha ya sata ya boye a kasashen ketare

- Buhari ya bayyana hakan ne a taron karawa juna sani na kasashen rainon Ingila reshen Afirka akan yaki da cin hanci da rashawa dake gudana a babban birnin tarayya Abuja

- Yace wannan shi ne sharadin da kasar Switzerland ta bayar yayin da take danka kudin ga Najeriya

A ranar Litinin, 14 ga watan Mayu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata rarrabawa yan Najeriya dala miliyan 320 wanda Abacha ya sata ya boye a kasashen ketare a lokacin da yake shugabancin kasa.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a taron karawa juna sani na kasashen rainon Ingila reshen Afirka akan yaki da cin hanci da rashawa dake gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo ya bayyana cewa wannan shi ne sharadin da kasar Switzerland ta bayar yayin da take danka kudin ga Najeriya.

A halin da ake ciki, a baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai sayarwa ‘yan kasuwa da wani bangare na kamfanin tatar main a Najeriya (NNPC), idan har ya zama shugaban kasa.

Atiku yayi bayanin cewa kamfanin na NNPC ya dade a cikin matsalar rashin kulawa a kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel