Buhari yayi ta’aziyya ga Fasto Bakare akan mutuwar mahaifiyarsa
- Buhari yayi ta’aziyya ga Fasto Bakare akan mutuwar mahaifiyarsa
- Shugaban kasar ya yi ta’aziyar tasa ne ta wayar
- Buhari ya bukaci limamin cocin da iyalansa da su yi hakuri
A ranar Litinin, 14 ga watan Mayu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziyya ga shugaban cocin Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare akan mutuwar mahaifiyarsa Misis Abigail Eebudola Bakare.
Shugaban kasar ya yi ta’aziyar tasa ne ta wayar tarho zuwa ga abokin nasa kuma abokin takararsa a shekarun baya.
Buhari ya bukaci limamin cocin da iyalansa da su yi hakuri duk da cewan marigayiyar Misis Bakare tayi tsawon rai da har taga nasarorin yayanta suka samu a rayuwa.
KU KARANTA KUMA: Zan karbi shawarar sauke ni da farin ciki – Kakakin majalisar jihar Kano
Shugaban kasar yayi kira ga iyalan marigayiyar da suyi riko da hallaya, karamci da taimakao irin na marigayiyar wacce ta mutu a ranar 5 ga watan Mayu, tana da shekaru 108 a duniya.
A halin da ake ciki, shugaba Buhari na a jihar Jigawa inda ya kai ziyarar aiki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng