Ramdan: Kungiyar JIBWIS reshen jihar Katsina ta rabawa malamai kayayyakin Azumi

Ramdan: Kungiyar JIBWIS reshen jihar Katsina ta rabawa malamai kayayyakin Azumi

- Kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus-Sunna (JIBWIS) a jiya ta rarrabawa malamai kusan 201 kayayyakin kusan N3m na shinkafa da Sikari gabanin shigowar watan Ramadan

- Ciyaman na kungiyar JIBWIS bangaren kwamitin Tafsiri, Khalid Ayyuba, yace hakan aniyi shi ne don karawa malaman kwarin gwiwa sakamakon tafiya da zasuyi zuwa wurare daban daban don gudanar da Tafsiri

- Ayyuba yace a shekarar data gabata kusan N7m aka samu ta hanyar kwamitin, wadanda akayi amfani dasu ta hanyar daukar nauyin Tafsirai a kafofin yada labarai

Kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus-Sunna (JIBWIS) a jiya ta rarrabawa malamai kusan 201 kayayyakin kusan N3m na shinkafa da Sikari gabanin shigowar watan Ramadan.

Ciyaman na kungiyar JIBWIS bangaren kwamitin Tafsiri, Khalid Ayyuba, yace hakan aniyi shi ne don karawa malaman kwarin gwiwa sakamakon tafiya da zasuyi zuwa wurare daban daban don gudanar da Tafsiri.

Ramdan: Kungiyar JIBWIS reshen jihar Katsina ta rabawa malamai kayayyakin Azumi
Ramdan: Kungiyar JIBWIS reshen jihar Katsina ta rabawa malamai kayayyakin Azumi

Ayyuba yace a shekarar data gabata kusan N7m aka samu ta hanyar kwamitin, wadanda akayi amfani dasu ta hanyar daukar nauyin Tafsirai a kafofin yada labarai.

KU KARANTA KUMA: Yadda jihohi 36 suka kasa N593.1bn daga watan Janairu zuwa watan Maris

Ayyuba, ya kara da cewa manufar JIBWIS shine kira ga addini musulunci zuwa ga duniya baki daya domin shine nauyin da ubangiji ya dora akan bayinsa.

A halin da ake ciki, shirye-shirye sun kankama domin fara azumin Ramadana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel