Tinubu Ya Kirkiro Sabuwar Hukuma a Najeriya, Ya Zabi Wanda Zai Zama Shugaban Farko

Tinubu Ya Kirkiro Sabuwar Hukuma a Najeriya, Ya Zabi Wanda Zai Zama Shugaban Farko

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar hukuma a Gwamnatin Najeriya tare da nada shugabanta na farko
  • Mai girma Tinubu ya nada Dr Obi Adigwe a matsayin shugaban farko na sabuwar hukumar wacce ta shafi harkokin kiwon lafiya
  • Hukumar za ta kasance karkashin Ofishin Ministan Lafiya, inda za ta jagoranci aiwatar da tsarin lafiya na zamani a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa Hukumar Fasshar Lafiya da Bayanai, 'National Health Technology and Data Analytics (NHTDAO).

Mai girma shugaban kasar ya kuma nada Dr Obi Adigwe a matsayin shugaban farko na sabuwar hukumar ta NHTDAO.

Shugaban kasa.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

An jingina barazanar tsaro ga galibin masu POS, EFCC za ta fara yaki da su

Sanarwar ta bayyana cewa sabuwar hukumar za ta kasance karkashin Ofishin Ministan Lafiya da Jin Dadin Al'umma, Farfesa Muhammad Ali Pate.

Ayyukan da aka dorawa hukumar NHTDAO

A cewar fadar shugaban kasa, NHTDAO za ta kasance cibiyar da za ta hada kai wajen tsara daidaitaccen tsarin fasahar lafiya ta zamani a Najeriya.

Sai dai an bayyana cewa hukumar ba za ta kwace ayyukan hukumomin lafiya na gwamnatin tarayya da ake da su ba, illa dai za ta hada kai da su domin kara inganta ayyukansu.

Haka kuma za ta aiwatar da da tsarin National Digital Health Architecture, wanda Majalisar Kula da Lafiya ta Kasa ta amince da shi a watan Nuwamban 2025.

Wanene Dr Obi Adigwe?

Kafin wannan nadin, Dr Obi Adigwe shi ne Shugaban hukumar da ke kula da harkokin cigaba da binciken magunguna wato NIPRD.

Ya jagoranci ayyuka da dama da suka shafi binciken kimiyya, fasahar kere-kere, amfani da fasahar AI da kuma wasu fasahohin zamani.

Haka kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsarin da ya taimaka Najeriya samun tallafin Tarayyar Turai na Euro miliyan 18 domin bunkasa binciken kimiyya.

Kara karanta wannan

Kano ta yi zarra, ta fi dukkan jihohin Najeriya sababbin masu rijistar katin zaɓe

A lokacin annobar COVID-19, Adigwe ya gudanar da binciken farko a duniya da ya karyata wasu ikirarin da ake yi kan maganin Covid Organics.

Dr Obi Adigwe.
Shugaban hukumar NHTDAO da aka kirkiro, Dr Obi Adigwe Hoto: Dr Obi Adigwe
Source: Twitter

Tinubu ya bayyana abin da yake bukata

A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu na sa ran sabuwar hukumar za ta hanzarta sauya tsarin kula da lafiya zuwa tsarin zamani mai amfani da bayanai, wanda zai kasance cikin tsaro, hadin kai da kuma inganta kiwon daukacin 'yan Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta ce wannan na daga cikin manufofin Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Bugu da kari sanarwar ta bayyana kwamitin gudanarwa na NHTDAO, wanda ya kunshi Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate a matsayin shugaba.

Tinubu ya nada sabon shugaban NUC

A wani labarin, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon Shugaban jami'ar UNILAG, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, a matsayin Shugaban hukumar NUC.

Shugaba Tinubu na sa ran Farfesa Ogundipe zai samar da nagartaccen shugabanci a NUC tare da tabbatar da ɗaga martabar jami'o'in Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta ce nadin na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke dauka domin karfafa tsarin ilimin jami'o'i da inganta nagartar ilimi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262