An hana kiran Sallah a birnin Kudus saboda bikin sauya wa ofishin jakadancin Amurka gari

An hana kiran Sallah a birnin Kudus saboda bikin sauya wa ofishin jakadancin Amurka gari

Gwamnatin Kasar Falasdin ta sanar da cewa, amfani da uzurin taruka wajen hana kiran Sallah a Birnin Kudus take hakkin Addini ne ga Musulmai.

Ministan Al'amuran Addini Kungiyoyi Yusuf Edis ya bayyana cewa, su ba suyi na’am da matakin hana kiran Sallah da gwamnatin Birnin kudus ta yi ba.

Edis ya ce, daukar wannan mataki ya zama kokarin rufe bakunan Musulman da ke birnin Kudus.

Ministan ya kara da cewa, wannan mataki da aka dauka a ranar da Amurka ke mayar da ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa Kudus ba abun amince wa ba ne kuma ba zai haifar da da mai ido ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi ta’aziyya ga Fasto Bakare akan mutuwar mahaifiyarsa

Gwamnatin Kudus ta sanar da cewa, sakamakon bukukuwan murnar mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa Kudus daga Tel Aviv ya sanya sun hana kiran Sallah a ranar Litinin a Kudus.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel